Yadda ake dafa-dukar shinkafa da daddawa
Shinkafa ta zama abinci gama-gari, amma hanyoyi daban-daban da ake da su na dafa masu gamsarwa, wata shinkafar ta fi wata. Ba maganar tuwon shinkafa da ko fara da miya ba, a’a, dafa-dukanta abinci ne da kwatancensa kadai, tun kafin ka ji kamshinsa, zai sa yawun mutum ya tsinke. Yadda ake hada ‘juice’ din kankana […]
Shinkafa ta zama abinci gama-gari, amma hanyoyi daban-daban da ake da su na dafa masu gamsarwa, wata shinkafar ta fi wata.
Ba maganar tuwon shinkafa da ko fara da miya ba, a’a, dafa-dukanta abinci ne da kwatancensa kadai, tun kafin ka ji kamshinsa, zai sa yawun mutum ya tsinke.
- Yadda ake hada ‘juice’ din kankana da abarba
- Abubuwa 10 kan Gimbiya Lolowah ’yar Sarki Fahd na Saudiyya
An yau mun kawo muku tsarabar wata shinkafa dafa-duka ta musamman, wadda ake yi da daddawa.
Abubuwa da ake bukatar
- Shinkafa
- Tumatiri
- Attarugu
- Daddawa
- Kifi
- Man ja
- Shuwaka
- Albasa
Yadda ake hadawa
- A dora tukunyar da ruwa a cikinta har sa ya tafasa
- sannan a dauko shinkafa a wanke a zuba a ciki,
- Idan ta dan tafasa kamar na minti 15 sai sauke a wanke da ruwa
- A yi jajjagen tumatir da attarugu da albasa da citta a ajiye a gefe
- Sai a wanke shuwakan da gishiri domin dacin ya fita
- A dora tukunyar a wuta a zuba manja a yankakken albasa a zuba ta soyu sosai
- Daga nan sai a zuba kifi ya soyu a kwashe kifin a zuba daddawa ya soyu
- A zuba jajjagen kayan miyar a ci gaba da soya shi
- A sa ruwa da sinadarin dandano da gishiri da kayan kamshi da shinkafar
- Daga nan sai a gauraya a rufe tukunyar na kamar tsawon minti 45
- Idan ta fara nuna sai a dauko wankeke shuwaka a zuba na tsawon minti
- Idan ya nuna sai a gauraya a sauke
A ci dadi lafiya.