Yadda ake dahuwar kaza ’yar China
Assalamu alaikum uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani sabon salon dahuwar kaza ’yar China. Tare da fatan uwargida za a gwada irin wannan ga maigida koda sau daya ne a wata. Ina son a sani cewa canja salon girke-girke na hana mutum cin girki iri daya. A […]
Assalamu alaikum uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani sabon salon dahuwar kaza ’yar China. Tare da fatan uwargida za a gwada irin wannan ga maigida koda sau daya ne a wata. Ina son a sani cewa canja salon girke-girke na hana mutum cin girki iri daya. A ci dadi lafiya.
Abubuwan da za a bukata
- Namankaza zalla marar kashi
- Albasa
- Abarba
- Garin masoro
- Ridi
- Barkono
- Magi
- Man gyada
- Tafarnuwa
- Soy sauce (ana samu a kantunan sayar da abincin zamani)
- Binegar
- Ketchup
Hadi
Bayan an wanke kazar sannan a yanyanka ta kanana. Bayan haka, a zuba garin masoro da magi sannan a ajiye a gefe. A dora tukunyar tuya a wuta sai a zuba man gyada kadan sannan a dauki wannan naman kazar a rika soyawa har sai ya yi launin kasa-kasa irin na soyuwa. Sannan a kwashe a ajiye a gafe.
A wannan tukunyar tuyar sai a zuba man gyada kadan da yankakkiyar albasa sannan a zuba soyayyiyar kazar a ciki ana gaurayawa na tsawon minti daya.
A samu wani kwano sai a zuba soy sauce din da wannan kazar a sake kwaba su. Bayan haka, a zuba ruwan abarba da barkono da garin tafarnuwa har sai sun nuna sannan a sauke.
Za a a iya hada wannan girki da jus mai sanyi. A ci dadi lafiya!