Yadda ake dahuwar kwai a cikin nama

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar kwai a cikin nama. Har ila yau ina dada ba ku shawara a kan girki mai armashi wanda zai sanya maigida ya manta hularsa da kuma hana shi cin abinci a waje. […]

Yadda ake dahuwar kwai a cikin nama

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na girke-girke.

A yau na kawo muku yadda ake dahuwar kwai a cikin nama.

Har ila yau ina dada ba ku shawara a kan girki mai armashi wanda zai sanya maigida ya manta hularsa da kuma hana shi cin abinci a waje.

Domin sauya irin nau’o’in abinci a koyaushe shi ya sa na kawo muku wannan sabon salon girkin. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata sun hada da:

  • Kwai
  • Ruwan qwai
  • Fulawa
  • Magi
  • Garin busasshen burodi
  • Nama/ ‘sausage
  • Kori
  • Man gyaxa

 

Hadi

A tafasa kwai har sai ya nuna sannan sai a bare.

Bayan haka, sai a samu ‘Sausage’ a kwaba shi da cokali.

Daga nan sai a wanke hannu a goge.

Sannan a zuba man gyada kadan a tafin hannu a dora nikakken naman sannan sai a shafe shi a tafin hannu.

A dauko dafaffen kwan sannan a lullube shi.

Bayan haka, sai a fasa kwai a zuba madaran ruwa kadan ko nono a kwaba, sannan sai a tsoma kwan a ciki.

Sai a samu fulawa a yaryada mata magi da kori a gauraya su sannan a saka kwan a ciki yadda fulawar za ta rufe kwan tsaf.

Bayan haka, sai a sake tsoma kwan a cikin ruwan kwan. A tsame sai a saka a cikin garin busasshen burodin yadda garin burodin zai lullube shi.

A zuba man gyada a wuta bayan ya yi zafi, sai a soya.

Sannan a tsame a sha da shayi.