Yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza

Barkanmu da warhaka uwargida da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza. Wannan irin dahuwar ana yi wa maigida ne a lokacin da zai dawo daga tafiya. Bugu da kari, domin burge maigida yin irin wannan girkin shi ya fi cancanta. Da […]

Yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza
Yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza

Barkanmu da warhaka uwargida da fatan ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar nikakkiyar kaza. Wannan irin dahuwar ana yi wa maigida ne a lokacin da zai dawo daga tafiya. Bugu da kari, domin burge maigida yin irin wannan girkin shi ya fi cancanta. Da zarar mace ta iya girki, zai yi wuya a ga maigida yana cin abinci a waje koda a gidan biki ne zai gwammace ya dawo gida yaci na uwargidansa. Don haka sai a dage mata!

Kayan hadi

•        Nikakkiyar kaza

•        Garin burodi

•        kwai

•        Fulawa

•        Attarugu

•        Garin tafarnuwa

•        Magi

•        Kori

•        Garin citta

•        Masoro

Yadda ake hadin

Uwargida ta samu kaza ta cire kashin jikin kazar sannan ta nika ta. Bayan ta nika, sai ta zuba a kwano. Sannan ta zuba dakakken masoro da kori da garin citta da magi da garin tafarnuwa da dakakken attarugu sannan ta cakuda su sosai.

Bayan an yi haka, sai a mulmula hadin sannan a sa a cikin fulawa sannan a sake shafa mata garin burodi sannan sai a zuba ruwan kwai sannan a jefa a man gyada mai zafi a tukunyar tuya. Bayan ta soyu sai a tsame. 

A ci dadi lafiya.