Yadda ake dahuwar shinkafa ’yar Senagal da kifi
Kayayyakin da ake bukata Shinkafa Karas Koren wake da tattasai Tattasai Attarugu Albasa Nikakken nama Sinadarin dandano Kori Tafarnuwa Citta Kifi Yadda ake girka Kalwale NDLEA ta kama ‘sarauniyar kwaya’ a Taraba Yadda za a girka shinkafar A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa. A dauko shinkafa a wanke a zuba […]
Kayayyakin da ake bukata
Shinkafa
Karas
Koren wake da tattasai
Tattasai
Attarugu
Albasa
Nikakken nama
Sinadarin dandano
Kori
Tafarnuwa
Citta
Kifi
Yadda za a girka shinkafar
- A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa.
- A dauko shinkafa a wanke a zuba a ciki.
- Idan ta dan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa, a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
- Daga nan sai a samu danyen nama a nika shi.
- A sake dora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyada a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
- Sannan sai a zuba nikakken naman a ciki a ci gaba da soya shi.
- Daga nan kuma sai a dauko citta da tafarnuwa da sinadarin dandano da kori sai a ci gaba da juya su, sannan a zuba su karas da koren waken da tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da murfi na tsawon minti 20, sannan a sauke shi.
- Sai a wanke kifi a ajiye shi.
- A zuba man gyada a tukunyar ya yi zafi, sai a soya kifi a ciki har sai kifin ya fara canja kala zuwa ruwan kasa kafin a cire ci daga wuta.