Yadda ake dahuwar shinkafa ’yar Senegal
Asalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa ’yar Senegal. Wannan shinkafar dai ba wata shinkafa ba ce illa shinkafar da aka saba dafawa a gida amma yadda ake sarrafa ta daban yake da yadda ake sarrafa shinkafa dafa-duka ko fara ko soyayyiyar shinkafa. […]
Asalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka shinkafa ’yar Senegal. Wannan shinkafar dai ba wata shinkafa ba ce illa shinkafar da aka saba dafawa a gida amma yadda ake sarrafa ta daban yake da yadda ake sarrafa shinkafa dafa-duka ko fara ko soyayyiyar shinkafa. Domin sake kwarewa dangane da sarrafa nau’o’in girke-girke, a juri karanta jaridar Aminiya bangaren girke-girke a kowane mako.
Abubuwan da ake bukata
- Shinkafa
- Karas
- Koren wake
- Tattasai
- Attarugu
- Albasa
- Nikakken nama
- Magi
- Kori
- Garin tafarnuwa da citta
Hadi
A dora tukunya da ruwa a cikinta har sai ya tafasa sannan a dauko shinkafa ’yar wara a wanke a zuba a ciki. Idan ta dan tafasa kamar na minti10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane. Sannan a samu danyen nama a nika shi. Naman ya kasance da dan yawa.
A sake dora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyada a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai. Sannan sai a zuba nikakken naman a ciki a ci gaba da soya shi sannan a dauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a sauke.
A samu salad a yayyanka a dafa kwai a zuba ‘cream` sannan a dora a ci, ita da jus din lemo.
A ci dadi lafiya.