Yadda ake dakile matan Arewa a siyasa —Barista Sa’adat
Tun a zaben fitar da gwani ake musu kafar ungulu in ma an bari sun say fom
Barista Sa’adat Yunusa Mohammad ’yar siyasa ce a Jihar Sakkwato da ta fito daga gidan sarauta, mai son ganin mata sun samu ’yancin da addini da al’ada ta ba su ce.
Saboda sha’awarta ga taimakon marasa karfi da gajiyayyu ta kafa gidauniya Sa’ar Mata Foundation don ta share hawayen marayu da mabukata.
A wannan hirar ta musamman, ta shaida wa Aminiya cewa ba ta da burin da ya wuri ta ga mata matasa suna iya dogaro da kansu.
Tarihinta
“An haife ni a cikin garin Sakkwato, na fara karatuna a makarantar firamare da ke kan Titin Birnin Kebbi.
Daga nan na tafi Sakandaren Gwamnatin Tarayya, bayan na kammala na wuce Jami’ar Usman Danfodiyo a Jihar Sakkwato inda na karanta fannin Shari’a.
Bayan nan sai na shiga makarantar horas da lauyoyi da ke Bwari Abuja.
Ni babbar lauya ce kuma babbar jami’a a Hukumar Kiyaye Hakkin Bil’Adama ta Kasa da ke Abuja.
Mene ne burinki na kuruciya?
Burina na kuruciya mai sauki ne, kawai ina son zama lauya, ga shi kuma yanzu na zama, duk da cewa ba abu ba ne mai sauki; kar ma ka ce makarantar horas da lauyoyi da gasa da kokarin tsere wa juna ya yanke cibi a can, ga shi dai ni yanzu lauya ce.
A ina kika hadu da mai gidanki?
Allah Ya kaddari na hadu da mai gidana a jami’a.
Ni dalibar koyon aikin shari’a ce a lokacin, tsangayarmu guda da shi a Jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato.
Kowane mutum yana da abubuwan da yafi sha’awa a rayuwarsa, a bangarenki wadanne iri ne?
Haka ne, daga cikin abubuwan da nafi sha’awa bai wuce tuki da yin iyo a ruwa ba.
Ya kike hutawa?
Ina gudanar da abubuwa da yawa a lokacin da nake hutuna; kamar karatu da sauraren Al-kur’ani, kuma lokaci ne da nake bai wa iyalina domin fito da abubuwa da za su taimaka wa rayuwarmu a yanzu har bayanta.
Barin wani abu da za a tuna ka da shi ba yana nufin ka bar dukiya ko gine-gine ko wani muhimmin abu da ake gani ba; sai dai barin wani abu mai amfani da zai rika tallafa wa rayuwar al’umma, da shi ne za a rika tuna ka, wannan shi ne ake nufi.
Wace shawarar kike da ita ga mata?
Mata na bukatar su hadu wuri daya su cure su yi riko da igiya daya.
Mata suna da ilmin da za su tafiyar da al’umma cikin karfafa juna da cigaba.
Shigar mata a harkar siyasa a matsayinsu na masu koyar da zaman lafiya da samar da natsuwa — don su jagoranci a cikin jininsu yake — abu ne da zai samar da cigaba a kasar nan ta wajen samar da shugabanci nagari da al’umma ke bukata.
Wane darasi kika koya a harkar siyasa?
Na koyi darussa masu yawan gaske a cikin harkar siyasa.
Mai girma a cikinsu shi ne na fahimci ba a bari a zabi mace a saman kowace kujera musamman a Arewacin Najeriya inda na fito.
Ka sani, a Arewa ba a kyale mace ta shiga tsundum a harkokin siyasa, ban san abin da hakan ke nufi ba, a ce ba a barin mu mu nemi kowace kujera a harkar siyasa.
Mu fada wa kanmu gaskiya, da zarar mace ta fito neman a tsayar da ita wata kujera, tun a wurin zaben fitar da gwani za a yi mata kafar ungulu in ma ta tsallake a wurin sayen fom.
Muna tare da kalubale babba, kan haka muke bukatar a samu wata jagora da za ta shiga lungu da sako ta fadakar da mata su san damar da suke da ita a siyasa, muna da wannan bukata kwarai da gaske.
Da wace mace kike koyi a rayuwarki?
Macen da kowa ke girmamawa a kasar nan: Sunanta Nana Asma’u diyar Usman Danfodiyo kaka ta ce, ’ya ce ga Mujaddadin addini da siyasa na Daular Sakkwato. Asma’u abar kwaikwayona ce kuma malamata ce.
Mene ne burinki na rayuwa a nan gaba?
Bani da wani buri da ya wuce na yi wa kasa da al’ummata hidima.
Kan haka nake son samun wata babbar kujera a cikin harkar siyasa don in ba da gudunmuwata a cigaban rayuwar mata da kananan yara.
Kana ganin a yanzu mun gamsu da rawar da ake takawa wajen cigaban mata da yara?
Ka san kam ba mu gamsu ba, dubi Majalisar Dokokin Kasa a misali, adadin matan da ke ciki sun yi kadan sosai.
Lokaci ya yi da ya kamata a bai wa mata dama su taka rawa a mukaman da maza suka mamaye, a gwada mata suma ba tare da wata kyara da hantara ba.
Me kike son a tunaki da shi bayan ba ki nan?
Ina son a rika tunawa da ni kan abubuwan amfani da na samar ga jama’a a lokacin rayuwata.
Abin da ke sanya a tuna da mutum ba kudi ko gidaje ko wasu muhimman abubuwa ba ne, sai dai abin da mutane ke amfana da ya shafi rayuwarsu.
Da shi ne kawai za su rika tunawa da kai, kuma wannan tunawar ce kowane mutum ke son a yi masa bayan baya nan.