Yadda ake fanken doya
Yadda ake fanken doya
Jama’a barkan mu da wannan lokaci. Yau a shafinmu na Girke-girken azumi za mu kawo muku yadda ake fanken doya.
Ga abubuwan da ake bukata domin hada shi:
– Doya
– Madara
– Fulawa
– Hodar ‘baking powder’
– Gishiri
– Kwai guda uku
– Bota
– Nikakken naman kaza
– Man gyada
– Tafarnuwa
– Albasa
– Attarugu
– Kayan dandano
Yadda ake hadin
- A dora man gyada a tukunya a wuta ba mai yawa ba, idan ya yi zafi sai a zuba yankakkiyar albasa, tafarnuwa da attarugu a ciki a soya na minti daya.
- A zuba nikakken naman kaza, a sa gishiri da kayan dandano, a motsa na tsawon minti 4 ko 5 sai a kashe wuta, a ajiye a gefe.
- A fere doya, a yayyanka ta, a wanke a dafa, idan ta nuna sai a daddaka a zuba a kwano mai zurfi.
- A zuba gishiri kaddan, da ‘baking powder’sai a juya sosai.
- A zuba fulawa da kwai sai a juya sosai, sannan a zuba hadin nikakken naman kazan a ciki.
- A zuba ruwan madara kadan-kadan har sai ya yi kauri daidai irin na fanke.
- Sai a dora tukunya mara kama girki a wuta, idan ta yi zafi a zuba bota kaddan, sai a rika debo kullun doya ana zuba shi ta irin yanayin da ake so.
- A bari ya nuna, sai a juya daya gefen shi ma ya nuna, sannan a kwashe.
Za a dinga haka daya bayan daya, har sai kullun ya kare. - Shi ke nan an hattama fanken doya, sai ci lafiya.