Yadda ake farfesun naman rago
Bayani dalla dalla kan yadda za a hada farfesun naman rago mai gamsarwa.
Idan maganar farfesu ake yi, na san za ku yarda cewa idan aka ambaci farfesun naman rago to sai dai kuma a ce kurunkus.
Uwa uba, naman ragon sallah da ragon dadinsa na daban ne, musamman idan ka samu soyayyensa ko tsire ko balangu da dai sauran hanyoyin da ake sarrafa shi.
- Yadda matasa 29 suka rasu a nutsewar jirgin ruwa a Sakkwato
- Hadarin mota ya kashe malaman da’awa 6 a Kano
Kusan duk mai mai son nama yana cin naman rago, kuma akwai hanyoyi daban-daban da ake sarrafa shi kamar farfesu da sauransu.
Shi ya muka kawo muku yadda ake yin farfesun naman rago, watakila za ku so samun shi a lokacin buda bakin azumin yau, ko kuma a wani lokaci.
Kayan hadi
- Naman rago
- Attarugu
- Albasa
- Citta
- Tafarnuwa
- Magi
- Kori
- krayfish
Yadda aka hadawa
Bayan a wanke naman sai a sa a tukunya a dora a wuta a sa sunadarin dandano, kori, tyme, gishiri, dakakken tafarnuwa da citta.
Kar a zuba ruwa har sai ya fara tafasa.
Idan naman ya fara laushi, sai a yi jajjagen albasa da attarugu da tafarnuwa da citta sai a zuba a cikin tukunyar.
Sannan a zuba ruwa, mangyada da dakakken crayfish da kayan kamshi, yadda ake bukata.
Daga nan sai a rufe tukunyar, bayan mintin 10 zuwa 15 sai a sauke
Za a iya cin wannan farfesun da shinkafa, doya, burodi ko ma tuwo.
A ci dadi lafiya