Yadda ake farfesun kan rago

Farfesun kan rago dadadden abincin marmari ne da ya zaga wurare daban-daban a fadin duniya kuma ake sha’awar shi. Bayan dadi a baki, farfesun naman kan rago ya kunshi sinadarai da ke tsaftace jini da kitse mai wuyar narkewa a jikin dan Adam. Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Yadda ake hada ‘juice’ din […]

Yadda ake farfesun kan rago

Farfesun kan rago dadadden abincin marmari ne da ya zaga wurare daban-daban a fadin duniya kuma ake sha’awar shi.

Bayan dadi a baki, farfesun naman kan rago ya kunshi sinadarai da ke tsaftace jini da kitse mai wuyar narkewa a jikin dan Adam.

Shi ya sa yau muka yi muku tsarabar yadda ake yin farfesun kan rago:

Kayan hadi

  • Gyararre kuma wankakken kan rago
  • Kayan kamshi
  • Sinadarin dandano
  • Markadaddiyar albasa
  • Attaruhu (daidai da yadda ake so)
  • Garin girfa kadan (cinnamon)
  • Dakakkiyar daddawa kadan

Yadda ake yi

  1. A wanke naman kan ragon a zuba a tukunya
  2. A zuba ruwa da duk kayan hadi sai a rufe tukunyar ruf
  3. A dafa tsawon mintina 40
  4. Idan aka taba aka ji ya yi laushi sai a sauke.

Ana ci da burodo, gurasa, ko shinkafa.

A ci dadi lafiya.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos