Yadda ake faten doya
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake faten doya. Faten doya dai girki ne wanda kowa ya san shi. Wani hanzari ba gudu ba, yadda wata za ta girka na ta daban da yadda wata matar za ta girka na ta faten doyar. Wata idan […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake faten doya. Faten doya dai girki ne wanda kowa ya san shi. Wani hanzari ba gudu ba, yadda wata za ta girka na ta daban da yadda wata matar za ta girka na ta faten doyar. Wata idan ta yi wannan girkin sai a ga doya daban da ruwa da manja ko kauri fatan bai yi ba. Sai a ga Manyan gobe ba su sha’awar cin abincin. Dole ne mata su dage da girka nau’ukan girke-girke yadda manyan gobe za su rage yin kwadayi idan an je unguwa.
Abubuwan da ake bukata
•Doya
• Manja
• Alayyahu
• Dakakken ‘cray fish’
•Albasa
• Attarugu
• Timatir
• Bandan kifi
• Nama
• Tafarnuwa
• Citta
• Magi
• Kori
Hadi
A samu Doya danya a fere, a yayyanka kanana sannan a wanke a ajiye a gefe. Bayan haka sai a samu ganyen alayyahu shi ma a yayyanka amma manya-manya a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A sulala nama da albasa da gishiri kadan sannan a sauke.
A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja sannan a zuba albasa da tafarnuwa da garin citta da yankakken attarugu da timatir. A yi ta gaurayawa har sai sun soyu. Sannan a zuba ruwan nama da naman da magi da kori a wanke bandan kifi a zuba da ‘cray fish’. Idan ya dan tafasa sai a dauko wannan doyar a zuba a ciki. Idan ta yi laushi sai a samu muciyar tuwo a dan faffasa doyar sama-sama yadda ruwan zai yi kauri sannan a dauko yankakken alayyahu a zuba na tsawon minti biyu zuwa uku. Idan ya nuna sai a gauraya a sauke. A ci dadi lafiya.