Yadda ake Faten Doya
Uwargida barka da rana. Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo yadda ake girka Faten Doya. Ga kayayyakin hadin da ake bukata: Tinubu na taro da Gwamnonin APC sa’o’i bayan ayyana takarar Tinubu Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Doya Manja Alayyahu Kifi (Cray fish) Albasa Attarugu Tumatir Kifi Nama Tafarnuwa […]
Uwargida barka da rana. Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo yadda ake girka Faten Doya.
Ga kayayyakin hadin da ake bukata:
- Tinubu na taro da Gwamnonin APC sa’o’i bayan ayyana takarar Tinubu
- Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali
Doya
Manja
Alayyahu
Kifi (Cray fish)
Albasa
Attarugu
Tumatir
Kifi
Nama
Tafarnuwa
Citta
to dandano
Yadda za a hada
A sami danyar doya a fere ta a yayyanka ta kanana-kanana, sannan a wanke a ajiye a gefe.
A zuba nama a tukunyar da albasa da gishiri har sai sun yi laushi.
A dora tukunya a wuta a sai zuba manja sanan a zuba yankakkiyar albasa da dakakke tumatir, attarugu, tafarnuwa da citta.
A yi ta gaurayawa har sai sun soyu.
Sai a zuba nama da romo da maggi.
A wanke kifi da crayfish a saka su, idan ya dan tafasa sai a dauko yankakkiyar doya a zuba a ciki har ta dahu ta yi laushi
Sai a samu ganyen alayyahu a yayyanka shi a wanke da ruwan gishiri sai a zuba a ciki
Idan ya nuna sai a gauraya a sauke.
[Idan an lura za a ga yawancin girke-girkenmu akwai tafarnuwa a ciki saboda tana magani sosai a jiki kuma tana fitar da kamshi a cikin abinci]