Yadda ake faten tsaki da gyada

Assalamu alaikum uwargida yaya yara? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Idan aka ambaci kalmar ‘fate’ nau’o’in fate da dama zai zo a tunaninmu. Akwai fate da dama da ake yi kamar: faten doya da faten wake da faten tsaki da sauransu. A yau za mu shiga gargajiya ce don haka za mu koya muku […]

Yadda ake faten tsaki da gyada

Assalamu alaikum uwargida yaya yara? Tare da fatar ana cikin koshin lafiya.

Idan aka ambaci kalmar ‘fate’ nau’o’in fate da dama zai zo a tunaninmu. Akwai fate da dama da ake yi kamar: faten doya da faten wake da faten tsaki da sauransu.

A yau za mu shiga gargajiya ce don haka za mu koya muku yadda ake faten tsaki da gyada. A sha fate lafiya.

Abubuwan da ake buqata

  • Tsaki
  • Kifi banda
  • Attarugu
  • Albasa
  • Tumatir
  • Alayyaho
  • Nikakkiyar gyada
  • Magi
  • Kori
  • Garin tafarnuwa
  • Garin citta
  • Manja ko man gyada

 

Yadda ake yin hadin

Da farko za a wanke tsakin masara ya zamo babu tsakuwa ko kadan sannan a dora tukunya a wuta a zuba manja ko man gyada sannan a yayyanka albasa a zuba da nikakken kayan miya a soya tare da bandar kifin.

A zuba magi da kori da garin tafarnuwa da na citta sannan a kwaba gyada kadan a zuba ta yi ta tafasa sannan a zuba tsaki har sai ya nuna.

A zuba tsakin kadan domin yana kumbura. Idan tsakin ya nuna sai a zuba yankakken alayyahon da aka riga aka wanke da ruwan gishiri kuma aka yayyanka.

Sannan sai a rage wutar risho. Bayan minti uku sai a sake gaurayawa a sauke.

A sha fate lafiya.