Yadda ake faten wake mai alayyahu
Kayan hadi Wake Manja Attarugu Tafarnuwa Albasa Tumatiri Gishiri Sunadarin dandano Alayyahu Yadda ake hadin A gyara waken a sa a cikin tukunya sannan a zuba ruwa a dora a wuta, sai waken ya yi kaman minti 45. A samu ganyen alayyahu a yayyanka a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe. A […]
Kayan hadi
- Wake
- Manja
- Attarugu
- Tafarnuwa
- Albasa
- Tumatiri
- Gishiri
- Sunadarin dandano
- Alayyahu
Yadda ake hadin
A gyara waken a sa a cikin tukunya sannan a zuba ruwa a dora a wuta, sai waken ya yi kaman minti 45.
A samu ganyen alayyahu a yayyanka a wanke da ruwan gishiri sannan a ajiye a gefe.
A yi jajjagen tumatiri, albasa, attarugu da tafarnuwa.
Bayan wake ya fara laushi, sai a sauke shi a wanke da ruwa a ajiye a gefe.
Daga nan sai a soya manja da albasa a tukunyar sannan a zuba jajjagen kayan miyar a ciki.
Bayan ya soyu sai a zuba wake da sunadarin dandano da gishiri a ruwan su dahu.
Idan waken ya fara laushi sosai sai a zuba yankakken alayyahu ya yi kamar minti uku zuwa hudu.
Daga nan sai a gauraya a sauke tukunyar.
Za a iya cin wannan girki shi kadai ko a hada da burodi ko garin kwaki.
Dabarun girki
- Idan abinci ya yi gishiri da yawa, a yayyanka dankali mitsi-mitsi a saka a ciki, anjima sai a cire shi, zai rage gishirin.
- Idan abinci kamar miya ta fara tsami, a sa baking foda da kayan dandano a ciki kafun a dumama.