Yadda ake gashin nama a Obin (Oben)
Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Yaya shirin Sallah? Tare da fatan za a yi kokarin gwada akalla daya daga cikin girke-girken da muke kawo muku. A yau na kawo muku yadda ake gashin nama a obin saboda Sallah da ke gabatowa ko za a gwada irin wannan gashin kuma […]
Uwargida barkanmu da warhaka tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Yaya shirin Sallah? Tare da fatan za a yi kokarin gwada akalla daya daga cikin girke-girken da muke kawo muku. A yau na kawo muku yadda ake gashin nama a obin saboda Sallah da ke gabatowa ko za a gwada irin wannan gashin kuma domin girka nau’o’in girki da dama domin burge maigida da kuma manyan gobe.
Abubuwan da za a bukata
- Nama
- Madara
- Albasa
- Lawashin albasa
- Tafarnuwa
- Gishiri
- Garin masoro
- Barkono
- Man Zaitun
- Kwai
Hadi
A kunna Obin ya yi zafi, sannan a samo kwano a kwaba madara sai a zuba garin masoro da jajjagen tafarnuwa da garin barkono da gishi da lawashin albasa sannan a gauraya sosai. Bayan haka sai a tsoma naman a cikin hadin sannan a zuba sauran hadin a cikin tire din Obin sannan a dora naman a ciki. Sannan a dauko dafaffen kwai a bare a yanka shi sai a saka a gefen naman. Sai a gasa na tsawon awa daya sannan a sauke a jira ya huce kafin a fara ci. A ci dadi lafiya.