Yadda ake girka Alalen Doya
Assalamu Alaikum Uwargida, barka da wannan lokacin. Yaya azumi?
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya
Assalamu Alaikum Uwargida, barka da wannan lokacin. Yaya azumi?
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi, za mu kawo muku yadda ake girka Alalen Doya.
- ’Yan bindiga Sun Yi A won Gaba da Budurwa A Zariya
- Bukukuwan Easter: An ayyana Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu
Da farko dai ga kayayyakin da uwargida ke bukata don yin alalen:
Doya
Manja
Man gyada
Attarugu
Albasa
Kifin karafish
Kayan kamshi
Kwai
Gishiri
Sinadarin dandano
Leda/gwangwani
Yadda ake yi:
Uwargida za ki fara gurza doya sai ki zuba albasa da atturugu a ciki ki markada.
Sai ki dafa kwai ki yayyanka shi ki ajiye a gefe.
Sannan ki sake yanka wata albasar ki zuba a kan markaden nan.
Sai ki dauko sinadarin dandano da gishiri da kayan kanshi da nikakken kifin karafish ki zuba a kai.
Daga nan sai ki zuba manja da man gyada a kai ki juya sosai.
Sannan sai ki dauko gwangwani ko leda ki rika zuba hadin alalen nan a ciki sannan ki dauko yankakken dafaffen kwai ki zuba a ciki.
Sai ki ajiye har sai kin gama sai ki zuba a tukunya yadda zai turara. Idan ya dahu sai ki sauke.
Shi ke nan alalen doya ya kammala.
A ci dadi lafiya.