Yadda ake girka burabusko da miyar taushe
Barkanmu da sake saduwa da ku iyayen gida a wannan fili namu na girke-girke. Kamar yadda ake cewa taba kidi taba karatu, haka kuma aka ce duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka nake ganin ya kamata mu koma gargajiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar taushe da […]
Barkanmu da sake saduwa da ku iyayen gida a wannan fili namu na girke-girke. Kamar yadda ake cewa taba kidi taba karatu, haka kuma aka ce duk wanda ya bar gida, gida ya bar shi. Don haka nake ganin ya kamata mu koma gargajiya. A yau na kawo muku yadda ake dahuwar miyar taushe da burabusko da man shanu. Tare da fatan za a rika gwada wa maigida. A sha karatu lafiya.
Abubuwan da ake bukata
- Garin burabusko
- Alayyahu
- Nikakkiyar gyada
- Magi
- Kori
- Garin tafarnuwa
- Man shanu
- Tantakwashi
- Manja
- Attarugu
- Albasa da tumatir
Hadi
A dora ruwa a wuta idan ya tafasa sai a rage wutar sannan a zuba garin burabusko ana gaurayawa sai a rufe da marufin tukunyar. A sake rage wutar sannan a jira kamar na tsawon minti 20. Sannan sai a kwashe da mara a sa a kwano a ajiye a gefe.
A silala nama da tantakwashi da albasa da gishiri kadan. Bayan haka, sai a jajjaga tumatir da attarugu. A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja idan ya yi zafi sai a zuba albasa idan albasar ta soyu sannan a zuba wannan jajjagaggen kayan miyar. A yi ta juya su har sai sun soyu.
A dauko nikakkiyar gyada a dama sannan a zuba romon naman da silalen tantakwashi a cikin kayan miyar. Bayan haka, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa sai a gauraya. Idan ya dan tafasa, sai a zuba kwababbiyar gyadar nan a cikin hadin kayan miya a sake gaurayawa.
A yayyanka alayyahu sannan a wanke da ruwan gishiri domin wanke datti da cututtukan da ke cikin ganyen. Sai a wanke kamar ruwa uku. A koma a sake juya miyar a kan wuta. A jira gyadar ta nuna sosai sannan a zuba wankakken alayyahu a rufe.
Bayan minti biyar, sai a sake gauraya miyar. Sai a sauke a dauko man shanu a soya da albasa sannan a zuba a kan miyar. Girki ya nuna! A dauko tuwon burabuskon nan a zuba masa wannan miyar a kai. A bai wa maigida.
A ci dadi lafiya!