Yadda ake girka farfesun Indomie mai kifi

Barkarmu da warhaka Uwargida. yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku sabon salon girka taliyar Indomie. A shekarun baya idan ba a manta ba na taba kawo muku wani salon girka Indomie wadda ake wanke shi kafin a zuba kayan hadi. A yau na kawo muku yadda ake […]

Yadda ake girka farfesun Indomie mai kifi

Farfesun Indomie mai kifi

Barkarmu da warhaka Uwargida. yaya yara? Tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku sabon salon girka taliyar Indomie. A shekarun baya idan ba a manta ba na taba kawo muku wani salon girka Indomie wadda ake wanke shi kafin a zuba kayan hadi. A yau na kawo muku yadda ake yin farfesunsa da kifi danye, tare da fatan za a dauki darasi kuma a gwada a gida don manyan gobe.

 

Abubuwan da za a bukata

•        Kifin karfasa/tarwada

•        Indomie

•        Attarugu

•        Albasa

•        Tafarnuwa

•        Ganyen kori

•        Magi

•        Kayan kanshi na girki

•        Karas

•        Lawashi

 

Hadi

Da farko za a wanke kifin yadda karnin zai fita sosai. Za a iya wankewa da ruwan kanwa ko toka domin rage karninsa. Bayan haka sai a zuba a tukunya sannan a zuba yankakkiyar albasa da jajjagen tafarnuwa da attarugu da magi sannan a zuba ruwa a cikin hadin.

Sai a dora a kan wuta a jira har sai kifin ya nuna sosai sannan a dauko taliyar Indomie a yi mata tafasa daya, sannan a dauraye da ruwan sanyi a tsane ta sosai sannan a zuba a cikin farfesun kifin, sannan a zuba  yankakken karas a ciki da lawashi da kuma ganyen kori.

Bayan ’yan mintuna kadan sai a sauke daga kan wutar a zuba a cikin kwano kamar na cikin kwanon.

A ci dadi lafiya!