Yadda ake girka kazar Indiyawa
Assalamu alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi […]
Assalamu alaikum Uwargida tare da fata ana cikin koshin lafiya. Kamar yadda na saba fada muku, yana da kyau idan za a yi girki a rika taba birni da kauye har da kasashen waje. Hakan ya sa a yau na dauko muku irin girkin mutanen Indiyawa ‘chicken curry’. Tare da fatan za a gwada shi wata rana ga mai gida ko kuma ga manyan gobe domin kara ilimantar da su a kan abincin kasashe waje.
Abubuwan da za a bukata
•Man zaitun
• Albasa
• Kori
• Madara (nonon da aka tafasa)
• Gishiri
•Dakaken masoro
•Heaby cream (za a iya samu a manyan shagunan da ke sayar da kayan girke-girke)
• Kaza daya
•Timatir guda daya.
•Ganyen kori.
Hadi
A wanke kaza sannan a silala ta da kayan kamshi da albasa da magi har sai ta yi laushi sosai. Sannan a sauke ta huce. A sami wuka a daddatsata kanana sannan a ajiye a gefe. A dora tukunya a wuta sannan a zuba man zaitun, idan ya yi zafi sai a zuba albasa sannan a yi ta juyawa kamar na tsawon minti bakwai sannan a zuba kori kamar cokali biyu na cin abinci, sai a ci gaba da juyawa na tsawon minti daya. Sannan a zuba tafasashiyar madara a cikin hadin tare da ‘cream’ da gishiri da magi da kuma yankakken timatir kanana sosai sai a ci gaba da juyawa. A dauko kazar da aka riga aka daddatsa a zuba a cikin miyar sannan a rufe na tsawon minti biyu kacal sannan a sauke. Za a iya sanya ganyen kori idan ana da bukata.
A tafasa farar shinkafa sannan a dauko hadin miyar Indiyawa a zuba a kan shinkafar tare da hada shi da jus din lemun zaki. Hmnnn! A ci dadi lafiya!