Yadda ake girka miyar agushi irin na Ibo

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar agushi kamar yadda Ibo ke girka nasu. Mata da dama na girka miyar agushi ta hanyoyi daban-daban. Wadansu ma zubawa kawai suke yi da sunan an yi miyar. Yana da kyau mace ta koyi yadda za […]

Yadda ake girka miyar agushi irin na Ibo

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar agushi kamar yadda Ibo ke girka nasu. Mata da dama na girka miyar agushi ta hanyoyi daban-daban. Wadansu ma zubawa kawai suke yi da sunan an yi miyar. Yana da kyau mace ta koyi yadda za ta rika canja salon girke-girke a koyaushe.

Abubuwan da za a bukata

  • Agushi
  • Manja /man gyada
  • Ganyen Uziza (za a iya samunsa a inda Ibo suke a kasuwa)
  • Tattasai
  • Albasa
  • Garin kifin ‘cry fish’
  • Daddawa
  • Kifi
  • Nama
  • Kayan dandano
  • Kayan kamshi

 

Hadi

A kwaba agushi da ruwa yadda zai dan yi kauri sannan a dora tukunya a wuta a zuba man gyada kadan da manja kadan. Bayan haka, sai a mulmula kwabin agushi zuwa kananan mulmule sannan a zuba albasa  a rika jefawa a cikin man. Haka za a rika jefawa sannan a juya da cokali na tsawon mintuna uku sai a zuba ruwa a cikin tukunyar da ake soya agushin. Sai a rufe da marufin tukunyan har sai ya tafasa sannan sai a dan farfasa agushin da cokali a zuba dafaffen busasshen kifi da dafaffan nama da  yankakken ganyen Uziza da kayan dandano da na kamshi sannan a rufe. Bayan mintuna goma zuwa sha biyu sai a sauke.