Yadda ake girka miyar koda
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana nan lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar koda. Akwai hanyoyi da dama da mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a rika karanta wannan shafi domin gano sirrikan girki […]
Assalamu alaikum Uwargida yaya yara? Tare da fatan ana nan lafiya. A yau na kawo muku yadda ake girka miyar koda. Akwai hanyoyi da dama da mata ke sarrafa koda. Walau a gasa ko a girka. Nawa salon girkin daban yake. Don haka yana da kyau a rika karanta wannan shafi domin gano sirrikan girki da kuma canja salon girki a koyaushe domin yara su rage kwadayi a makwabta.
Abubuwan da za a bukata
- Koda
- Albasa
- Tumatir
- Garin tafarnuwa
- Magi
- Kori
- Garin citta
- Attarugu
- Man gyada
- Koren tattashi
Hadi
A wanke koda ta fita fes. Sannan a yayyanka ta kanana sai a sanya ta a cikin tukunya tare da zuba mata ruwa kadan. Sannan a rufe. Idan ta fara nuna sai a yayyanka albasa da yawa a ciki a zuba yankakken tumatir da magi da garin tafarnuwa da garin citta kadan. Sannan a rage wuta sai a shiga gaurayawa. A zuba man gyada kadan sai a ci gaba da juyawa har sai albasa da tumatir da attarugu sun nuna. Sannan a kwashe a sanya a kwano. Sai a yayyanka danyar albasa da koren tattashi a zuba a kan kodar domin kawata girkin.
Za a iya cin wannan girki da dafa-dukar shinkafa ko kuma farar shinkafa da jus din lemun zaki.
A ci dadi lafiya.