Yadda ake girka miyar Oha

Yau a filinmu na Girke-girken Azumi, za mu kawo miki yadda ake girka Miyar Oha.

Yadda ake girka miyar Oha

Miyar Oha

Assalamu Alaikum Uwargida. Yau a filinmu na Girke-girken Azumi, za mu kawo miki yadda ake girka Miyar Oha.

Ga wasu daga cikin kayan hadin da ake bukata don yin miyar: 

Ganyen Oha

Gwaza kanana kamar guda takwas

Manja kamar cokali uku

Naman shanu

Kayan ciki

Ganda

Busasshen kifi

Barkono

Sinadarin dandano

Kifin ‘crayfish’

Yadda za a hada kayayyakin

A dafa kayan ciki da busasshen kifi da ganda ta yadda za su yi laushi.

Sannan a wanke naman shanu a zuba a tukunyar da kayan cikin ke ciki da sauran kifin.

A ci gaba da dafa su har sai naman ya nuna.

Sai a zuba sinadarin dandano kamar guda biyu sannan a ci gaba da dafawa na tsawon minti biyar.

Sannan a  zuba dakakken barkono da dakakken crayfish.

A ci gaba da dafa su na kamar tsawon minti 10.

Sai a tafasa  gwaza a kwaba ta a ruwa kadan a zuba.

A ci gaba da dahuwar  sannan a zuba manja a rufe tukunyar har sai miyar ta dan yi kauri.

Za a iya kara ruwan zafi idan miyar ta cika kauri sannan a gauraya.

Sai a tsinka ganyen na Oha da hannu kuma a yanka shi da hannu, ba da wuka ba domin kada  ganyen ya yi baki sannan sai a gauraya.

Za a iya cin wannan miyar da sakwara ko tuwon semovita.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos