Yadda ake girka miyar shuwaka
Assalamu alaikum uwargida! Barkanmu da sake saduwa da ke a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara cewa miya ita ce sirrin dadin tuwo. Idan har mace ta iya sarrafa miya da iri-iri, lallai kakarta ta yanke saka. Domin maigida ko tafiya zai yi sai ya yi […]
Assalamu alaikum uwargida! Barkanmu da sake saduwa da ke a cikin wannan filin namu na girke-girke. Kamar kullum dai ba zan fasa ba da shawara cewa miya ita ce sirrin dadin tuwo. Idan har mace ta iya sarrafa miya da iri-iri, lallai kakarta ta yanke saka. Domin maigida ko tafiya zai yi sai ya yi marmarin yin wannan tafiya da ita. Don haka ne a yau na kawo muku yadda ake miyar shuwaka. Tare da fatan za a gwada irin wannan girki don kwarewa a fannin girke-girke.
Abubuwan da za a bukata
• Ganyen Shuwaka
• Manja
• Naman shanu
• Kayan ciki
• Kifi banda
• Danyen kifin karfasa
• Magi
• Kori
• Kifin ‘cryfish’
• Attarugu
Hadi
A kankare fatar danyen kifin karfasa sannan a dora a wuta hade da magi da ruwa sannan a dafa har sai ya yi laushi sosai sannan a sauke. A cire kashin cikin kifin gaba daya, sannan a zuba a turmi a daka shi har sai ya yi laushi sannan a kwashe a ajiye a gefe.
A wanke naman shanu da kayan ciki a dora a kan wuta da gishiri kadan. Sannan a wanke bandar kifi a cikin ruwan zafi a cire kayar kifin.
Bayan naman da kayan cikin sun nuna sannan a zuba su a cikin tukunya tare da bandar kifin da kifin ‘cryfish’ da kuma dakakken kifinkarfasar. Sannan a dora wankakkiyar shuwaka a wuta da jajjagen attarugu da kori.
Sannan a gauraya su a zuba magi da manja. Idan ganyen shuwakar ya nuna sai a sake gauraya girkin a sauke. Za a iya hada wannan irin miyar da kowane irin tuwo.
A ci dadi lafiya!