Yadda ake girka miyar wake

A yayin da azumin watan Ramadana ya kan-kama, Aminiya za ta ci gaba kawo yadda ake yin wasu girke-girke domin magidanta su amfana. A yau mun kawo muku yadda ake yin miyar wake, wadda ana iya hada ta da abinci iri-iri musamman turo, sakwara, teba da sauransu. Ga abubuwan da ake bukata wajen girka miyar […]

Yadda ake girka miyar wake

Miyar wake

A yayin da azumin watan Ramadana ya kan-kama, Aminiya za ta ci gaba kawo yadda ake yin wasu girke-girke domin magidanta su amfana.

A yau mun kawo muku yadda ake yin miyar wake, wadda ana iya hada ta da abinci iri-iri musamman turo, sakwara, teba da sauransu.

Ga abubuwan da ake bukata wajen girka miyar wake:

Wake

Manja

Tumatir

Attaruhu

Tattasai

Bushenshen kifi

Albasa

Dunkulen sunadarin dandano

Kori

Gishiri

Yadda ake hadawa

Da farko za ki surfe wake ki wanke ya fita sosai, sai ki dora ruwa a wuta ya tafasa sai a zuba waken ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi taushi sosai

Sai a soya manja a wuta ya yi zafi sannan a zuba jajjagaggen kayan miya da albasa da manja da kifi.

Sai a sa maggi da kayan kamshi (kori da tyme) da gishiri, sai ki barshi yana turara har zuwa tsawon minti sha biyar.

Da zarar a duba miyar ta yi gwargwadon bukatar soyuwa sai a sauke

Za iya ci da tuwon shinkafa ko masara ko semobita ko waina.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Tags