Yadda ake girka sakwara da miyar kifi
Sakwara da miyar kifi kyakkyawan hadi ne da za a iya yi lokacin bude-baki
Uwargida barka da warhaka. Ya azumi? Yau a filinmu na Girke-girken azumi za mu kawo muku yadda ake girka sakwara da miyar kifi.
Sakwara da miyar kifi kyakkyawan hadi ne da za ki iya girka wa maigida da iyalanki lokacin bude-baki.
- Shin ya dace a kaurace wa zabe idan gwamnati ta gaza magance matsalar tsaro?
- Na samu sabon masallacin da zan ci gaba da limanci – Sheik Nuru Khalid
Ga kadan daga cikin abubuwan da za ki bukata domin girkin:
Doya
Kifi
Manja
Barkwano
Albasa
Magi
Kori
Tarfarnuwa
hadi
Uwargida ta fere doya sannan ta wanke ta dora a wuta har sai ta yi laushi
Sannan sai kibdauko turminki ki rika jefa dafaffiyar doyar kina dakawa har sai ta yi laushi.
Za ki iya zuba ruwan zafi domin sa sakwarar ta yi laushi.
Ki yanka albasa sannan ki daka barkono ya yi laushi sosai kuma ki wanke kifi sosai yadda ba za a ji karninshi ba.
Ki dora tunkunya a wuta sai ki zuba manja sannan ki zuba albasa ta dan soyu sannan ki zuba jajjagen tumatir har sai ya soyu, sai a zuba magi (kafi-zabo) da kori da tafarnuwa da kuma dakakken barkono.
Ki zuba kifin da ruwa kadan, sai ki rufe har kamar tsawon mintin 30, sai ki sauke.