Yadda ake girka shinkafa mai kwakwa
Assalamu alaikum warahamatullah, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake hada girkin shinkafa mai kwakwa. Da fatan uwargida na karuwa da filin namu na girke-girke da muke kawo muku nau’o’in kan girke-girke. Kayan hadi: • Shinkafa • Kwakwa • Karas • Koren wake […]
Assalamu alaikum warahamatullah, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake hada girkin shinkafa mai kwakwa. Da fatan uwargida na karuwa da filin namu na girke-girke da muke kawo muku nau’o’in kan girke-girke.
Kayan hadi:
• Shinkafa
• Kwakwa
• Karas
• Koren wake
• Fis
• Gishiri da magi kadan
Yadda ake yi:
Da farko uwargida za ta samu kwakwarta mai yawa sai ta goge bakin bayan nan sai ta goga rabi sannan ta markada rabin sai ta tace ta ajiye a gefe. Sai ta tafasa shinkafarta ta tace ta ajiye ta a gefe. Sai ta dauko kayan lambun nan da ta gyara ta tafasa su ta ajiye su a gefe. Sannan sai ta dora tukunya a wuta ta dauko ruwan kwakwar nan ta juye a ciki. Idan ya tafasa sai ta dauko shinkafar ta zuba a ciki. Sannan sai ta zuba gishiri da magi kadan tare da kayan lambun nan da ta tafasa da gurzajjiyar kwakwar nan a ciki, sai ta mayar da marufin tukunyar ta rufe. Idan ta dahu sai a sauke. Ana iya cin wannan shinkafar da miya.