Yadda ake girka ‘Sweet and Sour Shrimps’

Barkanmu da warhaka Uwargida, tare da fatan ana lafiya. Yana da kyau  idan an girka abincin gida Najeriya, kuma a taba na wadansu kasashe ba don komai ba sai don wayar da kan maigida da manyan gobe wajen sanin nau’ukan girke-girke saboda idan Allah Ya sa aka ziyarci wadannan kasashe ba za a yi bakunta […]

Yadda ake girka ‘Sweet and Sour Shrimps’
Yadda ake girka ‘Sweet and Sour Shrimps’

Barkanmu da warhaka Uwargida, tare da fatan ana lafiya. Yana da kyau  idan an girka abincin gida Najeriya, kuma a taba na wadansu kasashe ba don komai ba sai don wayar da kan maigida da manyan gobe wajen sanin nau’ukan girke-girke saboda idan Allah Ya sa aka ziyarci wadannan kasashe ba za a yi bakunta ba da irin girke-girkensu. Sanin girki wata fa’ida ce na ilmantar da al’umma. Wajibi ne uwargida ta koya wa ‘yan dugwui-dugwui  iya girki, domin idan sun kware sosai, za su iya bude wata makaranta ta koyar da wadannan girke-girken kuma hakan zai iya zamo musu sana’a a irin wannan yanayin da muka shiga na rashin samun aiki a kasa. A yau na kawo muku girkin Turawa “Sweet and Sour Shrimps’.

Abubuwan da za a bukata

  • ‘Shrimps’ (Ana iya samunsa a manyan shagunan da ake sayar da kaji ko kifi da suka yi kankara).
  • ‘Dark soy sauce (shi ma ana iya samunsa a manyan shagunan da ke sayar da kayan abinci).
  • Sugarin ko suga
  • Nikakkiyar citta
  • Cokali daya na nikakkiyar tafarnuwa danya
  • Rabin kofin ruwan abarba
  • Man zaitun
  • Karas
  • Attarugu
  • ‘Peas’ (za a iya samu a kasuwa inda ake sayar da su karas)

Hadi

Bayan ‘shrimps sun narke sai a tsoma su a cikin ruwan ‘dark soy sauce’ sannan a saka su a cikin gidan sanyi na tsawon awanni uku. Bayan haka, sai a tsame su daga cikin ruwan sannan a zuba suga da nikakkiyar citta da tafarnuwa da kuma ruwan abarba.

A dora tukunya a kan wuta sannan a rage wuta sai a dora tukunya wadda ba ta cika kama girki ba (non-stick) sannan a zuba man zaitun a cikin tukunyar daga nan sai a zuba wannan ‘shrimps din da aka tsame din a cikin man zaitun mai zafi sai a ci gaba da juyawa sannan a zuba yankakken karas a ciki, a ci gaba da juyawa har sai ta nuna sannan a sauke. Wannan irin girki ya dace da wadanda ke son rage kiba, domin yana dauke da sinadarin gina jiki.