Yadda ake girka tuwon shinkafa miyar ganyen Ugwu
Barkanmu da sake saduwa da iayaen gida tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Kamar yadda nake ba da shawarwari a kullum cewa yana da kyau mace ta koyi girki daban-daban musamman idan maigida ya kasance mai yawan son cin tuwo, to ya zama wajibi a kan mace ta koyi girka miya daban-daban ga maigida. […]
Barkanmu da sake saduwa da iayaen gida tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Kamar yadda nake ba da shawarwari a kullum cewa yana da kyau mace ta koyi girki daban-daban musamman idan maigida ya kasance mai yawan son cin tuwo, to ya zama wajibi a kan mace ta koyi girka miya daban-daban ga maigida. Idan ba ta koya ba, za a kawo mata wadda za ta zo ta koya mata wato abokiyar zama.
Kayan hadi
Tuwon shinkafa
• Shinkafar tuwo
• Ruwa
Hadi
A jika shinkafar tuwo a ruwa ta jika kamar na awa daya. Sai a dora ruwa a wuta bayan ya tafasa sai a wanke jikakkiyar shinkafar a zuba sannan a rage wuta a rufe da marufin tukunya. Bayan minti 20 zuwa 25 sai a sauke a tuka. A kwashe a leda sannan a ajiye a kwano wa maigida.
Miyar ganyen Ugwu
Abubuwan da za a bukata
• Ganyen Ugwu
• Ganda
• Kifi banda
• Albasa
• Tumatir
• Attarugu
• Magi
• Kori
• Manja
• Garin tafarnuwa
Hadi
A wanke ganda da ruwan zafi sannan a sanya a tukunyar dafa ganda a yanka albasa kadan da gishiri sai a rufe a dora a wuta. Bayan minti 40 sai a sauke a ajiye a gefe. A wanke ganyen Ugwun da gishiri da ruwa sannan a yayyanka a ajiye a gefe. A wanke kifi banda da ruwan zafi sannan a gutsura shi kanana a ajiye a gefe.
A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja bayan ya yi zafi, sai a zuba yankakkiyar albasa da tumatir da jajjagen attarugu a yi ta soyawa har su soyu. Bayan sun soyu, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da dafaffen gandar, bayan ya dan tafasa sai a zuba ganyen Ugwun a jira na tsawon minti uku zuwa hudu sannan a kwashe.