Yadda ake girkin faten acca
Uwargida barka da wanann lokaci a wannan filin na girke-girke. Ina fatar ana gwada irin girke-girken da muke kawo muku. Yana da kyau a rika sauya girki kayatar da iyali da kuma Karin dandano. A yau na zo muku ne da yadda ake yin faten acca. Kayan hadi: Acca Ruwa Allayahu Lawashin albasa Albasa Attarugu […]
Uwargida barka da wanann lokaci a wannan filin na girke-girke.
Ina fatar ana gwada irin girke-girken da muke kawo muku.
Yana da kyau a rika sauya girki kayatar da iyali da kuma Karin dandano.
A yau na zo muku ne da yadda ake yin faten acca.
- Kayan hadi:
- Acca
- Ruwa
- Allayahu
- Lawashin albasa
- Albasa
- Attarugu
- Magi
- Gishiri
- Kori
- Yadda ake hadawa
- A dora tukunya a wuta sannan a sanya acca daidai bukata a ciki idan ruwan ya yi zafi.
- Kar a saka acca da yawa saboda idan ta fara tafasa tana yin kauri.
- Sai a zuba yankakakkiyar albasa, alayyahu, lawashi da attarugun a ciki a juya.
- Bayan nan sai a zuba magi, gishiri da kori daidai bukata a juya sosai.
- Daga nan sai a bar shi a wuta ya dan turara kadan kafin a sauke.
Asha dadi lafiya.
Mulahaza: Sannan a rufe tukunyar har sai ya fara tafasa.