Yadda ake girkin Shurba

Shurba girkin Shuwa-Arab ne wadanda suke yawaita yin sa.

Yadda ake girkin Shurba

Shurba

Assalamu alaikum, a yau na kawo muku wani girki ne mai suna ‘Shurba.’

Shurba girkin Shuwa-Arab ne wadanda suke yawaita yin sa.

Yana da muhimmanci mu ci abubuwan da za su gina mana jiki a kowane lokaci.

Shurba wanda wasu Shuwa-Arab ke kira Marrara na magance cututtuka da dama a jikinmu.

Kamar ciwon sanyi ko mura da kuma zazzabi. Yana taimakawa wajen narkar da abinci da sauri a ciki da wanke daudar ciki, yana kuma taimakawa wajen dawo da marmarin abinci ga mutum mai jinya.

Girki kamar na Shurba yana mayar da ruwan jikinmu da ya ragu kuma kudi kalilan ya isa a girka Shurba da shi.

Abubuwan da za a bukata

  • Kayan ciki
  • Tafarnuwa
  • Albasa
  • Attaruhu
  • Man gyada
  • Kori da thyme
  • Sunadarin dandano
  • Citta
  • Gishiri
  • Ruwa
  • Nutmeg

Bayan an wanke kayan ciki, sai a soya man gyada da albasa.

Bayan sun soyu, sai a zuba kayan ciki ana gaurayawa, can sai a zuba ruwa daidai gwargwado, a zuba dakakkiyar tafarnuwa da yankakken tumatir da dakakken attaruhu da garin citta da garin Nutmeg da kori da thyme da magi daidai dandano da gishiri daidai misali.

Sai a jira ya yi ta dahuwa na tsawon awa daya. Bayan kayan ciki ya yi laushi sosai, sai a sauke a zuba a kwano don more rayuwa ko karbar baki.