Yadda ake gudanar da aiki a ofishin ’yan sanda mata zalla a Pakistan
Yan sanda mata a kasar Pakistan na artabu da masu laifi, kuma suna da ofishinsu na ’yan sanda mata zalla, a cewar babbar ’yar sandar kasar, Shazadi Gillani, wadda ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a wajen mahaifinta, lokacin da ta nuna sha’awar shiga aikin dan sanda.Sin feto Shazadi Gillani, wadda ta shafe shekara […]
Yan sanda mata a kasar Pakistan na artabu da masu laifi, kuma suna da ofishinsu na ’yan sanda mata zalla, a cewar babbar ’yar sandar kasar, Shazadi Gillani, wadda ta bayyana irin kalubalen da ta fuskanta a wajen mahaifinta, lokacin da ta nuna sha’awar shiga aikin dan sanda.
Sin feto Shazadi Gillani, wadda ta shafe shekara 19 tana aikin dan sanda, ta bayyana cewa, ta hakura da yin aure, sannan ita ta biya kudin da aka kashe wajen ba ta horon aiki. Kuma ita da kawarta Rizwana Zafar, wadda aka horar da ita tamkar da namiji, sun sha daga da masu aikata miyagun laifuka da ’yan tawaye.
A gundumar da Shazadi Gillani ke aiki, ’yan Taliban sun yi wa agarin kawanya, wato Khyber Pakhunkhwa. Tka ce ta kan sanya burka, tun daga kai zuwa idon sawu, ta kuma kare fuskarta da raga-raga, idan za ta yi tafiya. Ita kuwa Rizwana Zafar, ta kan yi gashin baki, tamkar namiji, sai ta rika yi mata rakiya.
Babban kalubalen da mata ke fuskanta shi ne yadda za a taimaka musu su shiga aikin dan sanda. Yawan ’yan sanda mata ya kai 560 daga cikin ’yan sanda dubu 60 da ke kasar. Shugabannin ’yan sand ana hankoron ganin wannan adadi ya nunka cbikin shekara daya, amma wahalar da ke tattare da aikin ke kawo musu cikas. An dai samu ’yar nasara a halin yanzu.
kasar Jamus ke daukar nauyin wuraren kwanan mata a kwalejoji uku da ake bayar da horo. Mata da ke shiga aikin dan sanda kan samu horo na tsawon shekaru. Mafi yawan matan Pakistan na fama da matsalar cin zarafinsu a gidaje, amma irin wadannan matan ba su son kai kara wajen maza, saboda al’adunsu sun kange su daga yawan magana da maza. Don haka a shekarar 1994 aka bude ofisoshin ’yan sanda mata zalla har biyu a gundumar.
Rozia Altaf, wadda ta shafe shekara 16 tana aikin dan sanda, ta ce sai da ta jira har shekara shida kafin a dauketa, kuma ta aike da takardun neman aiki, wanda yawansu ya wuce 50. Yanzu ita ce shugaba ofishin ’yan sanda na mata zalla da ke Peshawar, ta bayyana cewa an samu sauyi a halin yanzu. Kuma ofishinsu na Peshawar ya samu kararraki har 50 a bara.