Yadda ake gudanar da sha’anin mulki yau da kullum a Masarautar Zazzau
Tsarin gudanar da sha’anin mulki a Masarautar Zazzau nay au da kullum, ana gudanar da shi ne a cikin kwanakin mako bisa al’ada da kuma tsarin aiki irin na gwamnati. A Masarautar Zazzau akwai tsarin aiki na gwamnati wanda ake gudanar da shi kamar yadda ake yi a sauran ofisoshin gwamnati, akwai tsarin ma’aikata manya […]
Tsarin gudanar da sha’anin mulki a Masarautar Zazzau nay au da kullum, ana gudanar da shi ne a cikin kwanakin mako bisa al’ada da kuma tsarin aiki irin na gwamnati. A Masarautar Zazzau akwai tsarin aiki na gwamnati wanda ake gudanar da shi kamar yadda ake yi a sauran ofisoshin gwamnati, akwai tsarin ma’aikata manya da kanana wadanda gwamnati ke biyansu albashi kamar yadda take biyan sauran ma’aikatanta, don haka ne ake kiran masarautar a Ingilishi da Zazzau Emirate Council, wato Majalisar gudanar da Mulki ta Masarautar Zazzau. Wadannan manyan ma’aikata da kanana suna nan a Fadar Zazzau inda nan ne cibiyar masarautar Zazzau take da kuma wasu gundumomin mulki na hakimai da ke karkashin masarautar.
Haka kuma akwai ma’aikatan Sarki da wadansu masu yi wa Sarki hidima a cikin gida da waje wadanda ba gwamnati ke biyansu ba.
Ma’aikatan gwamnati a karkashin masarautar suna gudanar da aikinsu a cikin kwanaki biyar na aiki da gwamnati ta kebe su, sannan su huta a ranakun Asabar da Lahadi kamar yadda yake a tsarin aikin gwamnati. Sannan akwai ma’aikatan Sarki wadanda ba sa yin hutu ko wani tsari na aiki irin na gwamnati, hutunsu ko fara aikinsu ya danganta da fitowar Sarki da kasancewarsa a gari ko rashin zamansa a gari. Saboda haka ba su cikin tsarin kwanakin aiki na mako ko kwanakin hutun mako.
Ranar Litinin ta kowace mako Mai martaba Sarkin Zazzau yakan fito gida da misalin karfe goma sha biyu na rana (12:00) zuwa majalisarsa wato fadarsa tare da wadansu daga cikin fadawansa kamar Shamaki da Shantali da Sarkin Zagi da Majidadi da Sarkin Dogarai. Kafin Sarki ya fito yakan dauki lokaci a cikin gida don ya saurari jama’ar cikin gida da mata makusanta da ’yan uwa don gaisuwa ko jin koke-kokensu.
Bayan Sarki ya fito majalisa zai zauna, fadawansa na kusa wadanda suka fito da shi za su gaishe shi daya-bayan daya, daga nan Shamaki ko Shantali za su fada masa cewa akwai wadansu baki daga wani wuri ko daga wata masarauta. Bayan haka Shantali zai fito inda hakimai suke zaune a bisa jagorancin Wazirin Zazzau, zai fada wa Waziri cewa Sarki ya yi musu izini su shigo zuwa gaban Sarki, bisa tsar. Wazirin Zazzau yana gaba sai Galadima sai Fagaci sai Makama, sai Sarkin Fada sai Limamain Juma’a sai Limamin Kona da sauran ’yan Majalisar Sarki da hakimai kowa zai yi gaisuwa shi kadai a gaban Sarki, fadawa na fadin “GAISHE KA, SARKI YA AMSA.” Kowa zai zauna a wurin zamansa, kamar yadda muka ga tsarin a baya. Daga nan Sarkin Dogarai da dogarai, sai sauran fadawa da jami’ar gari, malamai da ma’aikata za a shigo da su bisa jagorancin Shamaki su yi gaisuwa daga nan Limamin Juma’a da Limamin Kona da Sarkin Ladanai da Na’ibi za su yi addu’a daya-bayan daya. Bayan sun kammala addu’a daga nan jama’a su tashi su yi gaisuwa daya bayan daya, Sarki yana amsawa.
Bayan an kammala gaisuwar fada sai hakimai su fara tashi suna sallama a gaban Sarki, fadawa na amsawa kamar haka. “Gaishe ka, Sarki ya Amsa” ana fadin sunan hakimin.
Mun samo wannan bayani ne daga shafin Facebook na: Kasar Zazzau A Jiya Da Yau