Yadda ake hada aure a Masallacin Abuja

Masallacin Area 11 da ke Abuja ya fara wani shiri na aurar da ‘yan mata da zawarawa ta hanyar cike fom da tantace maneman, har masallacin ya aurar da manema da yawa. Aminiya ta tattauna da ladanin masallacin kuma daya daga cikin masu jagorancin wannan shirin. Ga yadda hirar ta kasance:   Aminiya: Mene ne […]

Yadda ake hada aure a Masallacin Abuja

Masallacin Area 11 da ke Abuja ya fara wani shiri na aurar da ‘yan mata da zawarawa ta hanyar cike fom da tantace maneman, har masallacin ya aurar da manema da yawa. Aminiya ta tattauna da ladanin masallacin kuma daya daga cikin masu jagorancin wannan shirin. Ga yadda hirar ta kasance:

 

MasallaciAminiya: Mene ne tarihin wanna masallacin?
Sunana Malam Hamisu Alheri Dunkawa, ni ne ladani kuma mai jagorantar kula da masallacin Area 11. An kafa wannan masallaci ne tun a shekarar 1987, inda ake kiransa da suna Masallacin FCDA, sannan aka maida shi masallacin Juma’a, wanda ake kira da ‘Markazus-Sabirin,’ watau Masallacin Masu Hakuri na kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa Ikamatis Sunna (JIBWIS), ko kuma JIBWIS Islamic Learning Center Area II, Garki, Abuja.
 Aminiya: Yaushe kuka fara hada masu son aure?
 Asalin abin  ya faro ne bayan da shugabannin bangaren mata Hajiya Asama’u da Hajiya Jummai suka yanke shawarar cewa suna da yara da suka isa aure maza da mata, sannan sun tsara za a yi fom don cikewa a fahimci shekarunsu kafin a hada su su ga juna. Sai aka shaida wa Liman aka amince. Idan mutum ya zo karbar fom sai mu bincika ta hanyar malamai da ‘yan kungiyar Izala domin su aiko mana da halin wane, dan gidan wane. Idan an aiko cewa mutumin kirki ne, sai mu mu ba shi fom ya cika. Muna hada manema matashi da matashiya ko kuma bazawari da bazawara, da dai sauransu, amma ba ma yin gamin-gambiza, watu wacce ta yi karatu da wanda bai yi karatu ba.
 Aminiya: Daga wace shekara ak fara wannan shirin?
 A wannan shekarar aka fara wannan shirin.
 Aminiya: Mata nawa aka yi wa aure?
 An aurar da mata 20, watau mutane 40 suna cikin angawanci ke nan. Budurwa da wabanda suka taba yin aure.
 Aminiya: Nawa ne kudin fom din?
 Kyauta ne, amma kafin mu bayar sai mun tantance halin mutum mun san na kwarai ne. Kuma daga duk inda mutum yake muna iya sanin halinsa, ba sai lallai wanda ke zaune a Abuja ba.
 Idan yarinya tana wani gari ne, misali Birni Kebbi ko Kano, sai mu tura mutum ya je ya ganta, ba sai wanda ke Abuja ba. Amma duk wanda bai shirya aure ba kada ya zo, don ba mu yarda da dogon tadi ba.
Aminiya: Wadanne irin tambayoyi ake yi?
 Tambayoyin sune: suna da sana’a da shekaru, namiji ko mace da Jiha da lambar waya.
Aminiya: Mene ne mata suka fi nuna suna so?
Mata sun fi son mai addini, dogo, ba mai kiba ba kuma ba siriri ba, mai hankali. Amma ba duka aka taru aka zama daya ba. Wadansu sun fi son dattijo, don za ta zauna lafiya, domin samari sun cika karya da kawo mata ko neman mata a waje,da barin mace a gida a dawo mata cikin dare. Wata kumata fi son gajere, wata kuma ba ta son babban dan kasuwa, don ya cika yawon neman kudi a duniya, daga wanna kasa zuwa wancan kasa. Wata ta fi son mai addini, mai hankali, mai rufin asiri ba mai kudi da yawa ba. Wata ta fi son ma’aikaci, watau mai karbar albashi ba dan kasuwa ba. Wata kuma ta fi son mai kudi kafin komai ya biyo yaba.
Aminiya: Wacce mafi karancin shekaru kuka yi wa aure a wannan tsarin?
Wata budurwa ce ‘yar sheakar 20 wacce mahaifinta yake zaune a nan Area 11 kuma ta yi karatun boko.  
Aminiya: Wacce ce mafi yawan shekaru?
‘Yar shekara arba’in.
Aminiya: A maza wanne ne mai karancin shekaru?
dan shekara ashirin da biyu.
Aminiya; Sannan wanne ne mafi yawan shekaru?
 dan shekaru arba’in.
Aminiya: Shin lallai ne sai a nan Abuja ne za a daura auren?
 A’a ba sai a nan ba, idan ‘yar Sakkwato ce ta cika fom a nan Abuja, sai a daura mata aure a can Sakkwato. Idan kuma ‘yar Abuja ce sai a yi a nan.
Aminiya: Shin kuna yi musu hudubar zaman aure kafin a yi auren, kuma idan an samu rashin jituwa yaya kuke yi?
 Lallai muna yi musu huduba da cewa aure ibada ce. Kuma a yi hakuri, idan yau ba a samu abin duniya ba, gobe  za a samu, idan ana nema da hakuri da gaskiya.
Aminiya: Fom nawa kuke da su wadanda aka cika a yanzu haka?
Muna da fom da aka cika har guda 70. Na mata 40, na maza 30.
Aminiya: Idan akayi haduwar farko ba a fahimci juna ba, yaya kuke yi?
 Idan yarinya ta gaya mini, sai in gaya wa wanda ya je wurinta, sai mu nema mata wani.Haka shi ma idan ba ta yi masa sai a nema masa wata.
Aminiya: Wane abin mamaki ya taba faruwa ga maneman?
 Wani ya je wurin wata yarinya zuwan farko, amma ya ki komawa. Da na bincika, sai ya ce ai gidan nasu ya cika girma , watau masu kudi ne matuka. Sannan yarinyar ta yi masa kwalliyar da ta wuce hankalinsa, don ta sa gwala-gwalai da suka firgitashi. Amma an lallabe shi ya dawo a daidaidata. Ya ce motarsa ba ta isa a je cefane da ita a gidan ba.
 Ina  ba mata sharawa da su san cewa arziki na Allah ne, domin yawanci an haife su ne a Abuja, sun yi kararu a Abuja, sannan sun fi son su yi aure a cikin birnin Abuja, don ba sa son fita wajen gari, kamar Maraba ko Nyanya da sauransu. Su kuma iyaye ya dace su rika zumunci sosai, don idan an shigo Abuja ana zaune ne inda ba a cika samun jama’a ba balle a samu masoyin da za a iya yi aure da shi. Akwai kuma mata da ba ma fatan su zo karbnar fom a na. Don akwai wacce take son ta auri wanda ya shahara kamar Minista, ko babban ma’aíkaci da ya yi suna. Muna fata mata su yi aure su kuma ci gaba da neman halal, don ba komai ake nema, ake samu ba.