Yadda ake hada baki da ’yan uwa a sace mutane a Zariya

’Yan sanda sun cafke kimanin mutum 30 masu irin wannan muguwar dabi’a.

Yadda ake hada baki da ’yan uwa a sace mutane a Zariya

wani yaro an rufe masa baki da hannu. (Hoto: Shutterstock)

Yadda ’yan uwa da makusanta ko amintattu ke kitsa yadda ake sace ’yan uwansu a yi garkuwa da su don karbar kudin fansa na kara yawaita a yankin Zariya.

Runduna ta musamman da ke yaki da ayyukan ta’addanci da satar mutane da ke ofishin shugaban ’yan sanda (IRT) a Jihar Kaduna ta shaida wa manema labarai cewa ta kama kusan mutum 30 wadanda aka hada baki da su aka yi garkuwa da ’yan uwansu da makusantansu.

  • SAURARI: Yadda Zamfarawa da Kanawake barin gida saboda rashin layin sadarwa:

Da yake bayani kan irin wannan mummunar dabi’a, wani jami’in IRT da ya bukaci aka boye sunansa, ya ce, “Mun kama mutanen da ake hada baki da su a kama ’yan uwansu a yi garkuwa da su, cikinsu har da wanda yake da ban mamaki kamar wani da aka hada baki da shi… kuma shi ne mijin matar da aka sace”.

Daga cikin masu irin wannan hadin baki da asirinsu ya tonu a yankin Zariya, tun daga bara zuwa yanzu har da wani wanda aka hada baki da shi aka sace matar yayansa, a unguwar Makada da ke Dutsen Abba.

  1. – Yaiwatar hada baki a sace ’yan uwa

Shi ma wani mazaunin Layin Mahauta a Tudun Jukun, wanda ya sace dan makwabcinsa ya yi garkuwa da shi har ya karbi kudi Naira dubu 50, dubunsa ta cika.

Sannan akwai wani magidanci da ke zaune a makarantar marigayi Malam Kasim da ke Kofar Gayan Zariya da shi ma dubunsa ta cika.

Akwai jami’in tsaron Jami’ar Ahmadu Bello, da aka hada baki da shi aka sace ma’aikatan jami’ar.

Sannan akwai wani kuma wani da aka hada baki da shi aka sace uban gidansa da ke a tsallaken Dogo da ke Wusasa Zariya.

Bayan shi akwai wani wanda aka hada baki da shi aka je aka sato yayansa da suke uwa daya uba daya, a kauyen Madani da ke ’Yan Kara a Jihar Katsina, aka karbi kudin fansa Naira dubu 45 aka ba shi Naira dubu shida a cikin kudin.

A baya-bayan nan, an kama wani matashi mai shekara 35, mazaunin unguwar Magumai da ke gundumar Tukur Tukur Zariya, wanda ya hada baki aka sace yayarsa bayan ta ba shi Naira miliyan daya da dubu dari hudu ya ja jari; Amma ya hada baki da masu satar mutane aka sace ta aka kaita kauyen Galadimawa aka tsareta a can.

  1. – Abin mamaki

Jami’in Rudunar IRT da muka zanta da shi ya ce akwai wani wanda aka hada baki da shi aka yi garkuwa da surukinsa saboda yafi shi shanu, amma dubunsa ta cika.

“Aka karbi kudin fansa har aka ba shi ba shi jarin Naira dubu dari da hamsin, kuma mun gabatar da shi a gaban kotun majistire na 3 da ke Barnawa wanda mai shari’a Shamsuden Jafaru ke shari’a.

“Sai kuma wanda ya gayyato barayin shanu aka zo gidansu aka kwashe shanun gidansu a Saubawa a garin Rigacikum har aka kashe yan uwansa biyu.

“Sai wani direba mazaunin unguwar Kofar Kibo Zariya da ya gayyato wasu suka sace dan uwansa mai aka yi garkuwa da shi.

“Sai wani yaron gida da ke anguwar Madaci shi ma aka hada baki aka sace maigidansa.

“Sai wannan na karshen wanda muka kama mazaunin anguwar Magumai wanda aka hada baki da shi aka sace yarsa.

“Duk wadannan mun kama su, kuma wasu suna gaban shari’a, wasu kuma suna tsare domin wadanda aka sace ba su dawoba, don haka muke tsare da su har sai mun kammala bincike.

Muna kira ga al’umma da su daina saurin yarda ko saurin amincewa da mutane a wannan lokacin, ganin yadda aminci ko amana ta yi karanci.

  1. – Dalilin hada baki a yi garkuwa da makusanta

Wani mai sharhi da kuma bibiyar al’amuran yau da kullum, Sani Aliyu, wanda kuma dan jarida ne ya ce son zuciya da neman duniya ko ta halin kaka suna daga cikin dalilan da mutanen suka zabi wannan mummunar dabi’ar a matsayin mafita a garesu.

Wani mazaunin Zariya, Halliru Hamza Kakaki, ya ce abin da ke kawo a hada baki da dan uwa ko amintacce a sace wa makusancinsa shi ne rashin Imani.

“Kai bama wai a saci dan uwa ba, har ma wanda ba dan uwa ba dan a karbi kudi ai rashin imani ne da kuma rashin tausayi na mutanen da zuciyarsu ta kekashe, domin ba wai rashin aiki ke kawo yin haka ba a’a, kusan duk wadanda aka kama da irin wannan cin amanan za ka ga ai suna da abin yi sai dai ko ace rashin godiyar Allah.

“Kuma abin da ke kara kawo haka shi ne rashin hukunta su a fili kowa ya gani shi ne ke kara yawan aikata hakan,” a cewersa.

Shi kuma Malam Balarabe Tanko Tukur Tukur, cew ya yi, “Ai abin da ke kawo hadin baki da dan uwa ko da a sace uba ko a sace dan uwa shi ne gaggawa na rashin hakali wajen ganin cewa an kai wajen da lokaci bai yi ba ko bakin cikin kana da shi ni bani da shi.”

Ya kara da cewa, “Kuma ya kamata mutane su sani cewa ko dan da ka daifa da cikinka zai bar gida ba tare da ya sanar da kai ba har na tsawon wani lokaci sai ya dawo, to kada ka yi saurin amincewa da shi. Ballantana wanda hulda ce kawai ta hada ku da shi

“Abu na karshen shi ne irin soyayyar son zuciya da ake nunawa da kuma kin bin gaskiya da cin hanci da rashawa, duk su ne musabbabin irin wadannan fitina.