Yadda ake hada ‘Fruity Zobo’

Assalamu alaikuma jama’a, yau na kawo muku yadda ake hada Fruity Zobo. Hadin Zobo ne na musamman da za a iya yi domin sha a gida ko taro ko kuma sayarwa. Ga yadda ake hadawa: Abubuwan da ake bukata Zobo Sukari Abarba Lemo Gurji (cucumber) Karas Citta Kanumfari Flavor Yadda ake hadawa A dora ruwa daidai […]

Yadda ake hada ‘Fruity Zobo’

Assalamu alaikuma jama’a, yau na kawo muku yadda ake hada Fruity ZoboHadin Zobo ne na musamman da za a iya yi domin sha a gida ko taro ko kuma sayarwa. Ga yadda ake hadawa:

Abubuwan da ake bukata

  • Zobo
  • Sukari
  • Abarba
  • Lemo
  • Gurji (cucumber)
  • Karas
  • Citta
  • Kanumfari
  • Flavor

Yadda ake hadawa

A dora ruwa daidai bukata a tukunya ya tafasa, sannan a saka bawon abarba a ciki.

Sai a dauko gyararren citta da kanunfari a zuba a ciki daidai bukata.

Daga nan sai a sa yankakken gurji da lemo a ciki a bari ya yi ta tafasa na minti 15 zuwa 20.

Bayan nan sai a zuba zobon a ciki tafashehen ruwan a bar shi na tawon minti 15 kafin a sauke.

Idan ya huce sai a dauko ruwan nikakakken karas da abarba da gurji da aka riga aka tace a sanya a ciki.

A tabbata sun niku sosai an kuma tace da kyau. Za kuma a iya yin su daban-daban ko a hade.

Daga nan sai a sanya flavor cikin chokali da sukari juya sosai.

Za a iya sanya inabi ko yankaken gurji a ciki in ana bukata.

Sai a je a saka a fridge a bari ya yi sanyi ko kuma a saya kankara a ciki – gwargwadon bukata.

Wannan shi ne yadda ake hada Fruity Zobo.

A sha Fruity Zobo lafiya.

Tags