Yadda ake hada garin dilke mai gyara jiki
An fi sanin mutanen Barno wurin amfani da garin dilke don gyaran jiki. Hakan ne ya sanya a wannan makon muka kawo muku yadda ake hada dilke. Yawanci ana amfani da garin dilke ne wurin gyara wa ‘yan matan da suke shirin zama amare jiki, akan yi hakan ne kafin a yi bikinsu. Akwai hanyoyi […]
An fi sanin mutanen Barno wurin amfani da garin dilke don gyaran jiki. Hakan ne ya sanya a wannan makon muka kawo muku yadda ake hada dilke. Yawanci ana amfani da garin dilke ne wurin gyara wa ‘yan matan da suke shirin zama amare jiki, akan yi hakan ne kafin a yi bikinsu. Akwai hanyoyi da dama da ake hada dilke; akwai na dankali da na gyada. Shafa dilke a jiki na taimakawa wajen cire fatar da ba ta da amfani a jikinmu kuma yakan sa fata ta yi laushi da santsi da kuma kyalli.
Abubuwan bukata:
Gyada da man zaitun da ruwa.
Hadi:
A nika danyar gyada tare da bawonta, sannan a wanke ta da ruwa, daga nan zuba ta a matsami, sannan a soya ta da mai kadan har sai ta canza launi zuwa ruwan kasa.
Yadda za a shafa:
A tafasa ruwan zafi, sannan sai a kwaba garin dilke da mai kadan har sai hadin ya yi kauri. Bayan hakan, a jika fatar jiki da ruwan dumi kafin a fara shafawa da tafin hannu. Bayan an gama dirza dilke a fata an cire dattin fata, sai a wanke da ruwan dumi. A bar jiki ya bushe kafin a shafa man shafawa.