Yadda ake hada kazar ‘chicken balls’
Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Masu karatunmu da dama na ta tura mana sakonnin cewa a sake yi musu bayani kan wannan girki na ‘chikin balls.’ Don haka a yau na sake kawo muku yadda ake hadawa tare da fatan za a sa ido domin ba mu cika son komawa baya […]
Barkanmu da warhaka uwargida tare da fatan ana lafiya. Masu karatunmu da dama na ta tura mana sakonnin cewa a sake yi musu bayani kan wannan girki na ‘chikin balls.’ Don haka a yau na sake kawo muku yadda ake hadawa tare da fatan za a sa ido domin ba mu cika son komawa baya ba. Domin kada wani girki ya wuce ki, sai a ci gaba da sayen jaridar Aminiya a kowace juma’a. A sha karatu lafiya.
Kayan hadi
- Kaza
- Kwai
- Dankalin Turawa
- Magi da gishiri
- Tattasai da attarugu da albasa
- Man gyada
- Kori ‘Curry’
Hadi
Idan uwargida ta wanke kazarta tas, sai ta tafasa ta da dan gishiri da albasa har sai ta yi laushi sosai, sannan a cire kasusuwan da ke jikin kazar. A dafa dankalin Turawa ya dahu sosai sannan a ajiye shi a gefe. A markada tattasai da attarugu da albasa. Bayan haka, sai a tsoma dafaffen dankalin tare da kazar a cakuda su da magi da gishiri da kuma curry. Sannan a fasa kwai a kan hadin da aka yi. Sai a mulmula su daya bayan daya. Sannan a dora man gyada a wuta a tukunyar tuya a soya su. Bayan sun soyu sai a sauke.
Himm dadi! Wannan irin girkin ba a bai wa mai kyuya. Za a iya cin wannan girki da safe.