Yadda Ake Hada Lemon Na’a-Na’a Da Kokumba
Hada wadannan abubuwa biyu a waje guda ba karamin lafiya zai kara wa jiki ba
Gurji, wanda aka fi sani da Kakumba, da Na’a-na’a nau’in kayan abinci ne da suka kunshi sinadarai masu amfani sosai ga lafiyar jikin dan Adam.
Kakumba na dauke da wadataccen ruwa a cikinsa, da ke taimakawa wajen rage kiba da bai wa jiki ruwan da yake bukata.
A hannu guda kuma na’a-na’a na taimaka wa jiki magance matsalolin magwas da kumburin ciki tare da taimaka wa kwakwalwa da kuma hana warin baki na larura.
Kun ga ke nan hada wadannan abubuwa biyu a waje guda, ba karamin lafiya zai kara wa jiki ba.
Kayan hadi:
- Na’a-Na’a
- Kokumba
- Dafaffen sukari/Syrup
- Filebo
Yadda ake yi:
- Da farko a samu Na’a-na’a koriya sosai sai a wanke ta tas.
- Sai a markada ta daga nan sai a tace a ajiye ruwan a gefe guda.
- A samu Kokumba mara daci a yayyanka ta a markada a tace.
- Sai a dafa sukari har sai ya narke ya zama tsararo (syrup).
- A juye tattaccen ruwan Na’a-Na’a da na Kokumba a kofi.
- Dag nan sai a dauko syrup din a zuba a kan hadin.
- A zuba filebo na ruwa, dandanon da ake so, a ciki.
- Sai a sa a firiji, ko a jefa kankara a ciki, idan ya yi sanyi sai sha.