Yadda ake hada man hana zubewar gashi
Wannan man yana kara wa gashi lafiya, cika da kuma tsayi.
Mata da yawa na fama da zubewar gashi ko karyewarsa, saboda dalilai daban-daban, kuma asarar gashi abu ne da ke ci wa mata da yawa tuwo a kwarya, musamman saboda suna son ganin gashinsu da tsayi.
Shi ya sa muka kawo wannan hadi da zai taimaka muku wajen rage zubewar gashi.
Wannan man yana kara wa gashi lafiya, cika da kuma tsayi.
Kayan hadi:
- Kanamfari
- Man kwakwa
- Tafarnuwa
- Albasa
Yadda ake hadin:
A bare tafarnuwa da albasa, a daka su tare, a zuba kanamfari a daddaka duka.
A samu kwalba mai fadin baki a zuba kayakin da aka daka, sai a zuba man kwakwa ishasshe a ciki.
A zuba dakakkiyar tafarnuwa da albasa da kanamfari a ciki, sai a jijjiga sosai sai a ajiye tsawon kwana uku.
Bayan kwana uku, sai a kara jijjigawa sosai sannnan a tsatse man a zuba a mazubin da ake so.
Shi ke nan sai a dinga shafawa a gashin a fatar gashi a kai a kai.
Wannan man na gyaran gashi sosai.