Yadda ake hada man kwakwa

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin na mu na kwalliya. Man kwakwa na da muhimmanci kwarai a jikinmu domin ana amfani da shi wajen gyaran fata da gashi da kuma tafin kafa. Kamar yadda nake rubuto muku ababen gyaran jiki, za a ga yawancin kayan hadin na kunshe ne da man kwakwa. […]

Yadda ake hada man kwakwa

Barkanmu da sake kasancewa da ku a wannan filin na mu na kwalliya. Man kwakwa na da muhimmanci kwarai a jikinmu domin ana amfani da shi wajen gyaran fata da gashi da kuma tafin kafa. Kamar yadda nake rubuto muku ababen gyaran jiki, za a ga yawancin kayan hadin na kunshe ne da man kwakwa. Bisa ga irin kira da nake samu a wajen mutane don yadda za su sami man kwakwa, wasu ko sun je kantuna ba sa samu, shi ya sa a yau na ce bari na kawo muku yadda ake hada wannan man domin samun fata mai laushi da gashi mai tsayi da laushi da kuma tafin kafa mara kaushi. A sha karatu lafiya.

Ababe da za’a bukata
•Kwakwa
•Ruwa
Yadda za a hada
A kankare bayan kwakwa ya rage farin kawai. Sannan a yanyanka ta kanana saboda ta yi saukin nikawa.
A zuba ruwa da dan dama a cikin blandar sai a hada da yankakkiyar kwakwa. Sai a nika har sai markaden ya yi laushi sosai.
A sami a bin tatan kamu a tace ruwan kwakwa sosai. Za a ga ruwan kamar madara.
Za’a iya ajiye markadadden ruwan kwakwa na kwana daya ma ga wadda ba ta da firiji. Ko kuma a saka shi a firiji domin ruwan ya hadu sosai.
Bayan kwana daya za a ga madarar kamar kindirmo a saman kwano. Sai a kwashe wannan madarar da aka tace a zuba ta a cikin tukunyar suya.
Sai a dora tukunyar a kan wuta. Haka za a yi ta juyawa da cokali har sai wannan madarar ta koma kamar ruwan kasa mai dan duhu.
Sai a sauke a sake tacewa. Za a ga man kwakwar ya fito tsaf. Sai a sami kwalba a ajiye ana amfani das hi yadda ake so.
Yadda ake hada man kwakwa-Amina Abdullahi