Yadda ake hada Meat Pie
Ana ba uwargida shawarar kada ta bar gidanta ba komai saboda bakin ba-zata.
Cimakar Meat Pie na daya daga cikin kayan taba-ka-lashe kuma na karbar baki.
A kullum ina ba uwargida shawarar kada ta bar gidanta ba komai saboda bakin ba-zata.
- Takardun Pandora: Asirin wasu shugabannin duniya ya tonu
- Majalisar Malaman Kano ta sauke Sheikh Ibrahim Khalil kan ‘ci da addini’
Za a iya hada wannan abin makulashe ne a lokacin bukukuwa kamar Sallah ko bikin radin suna ko kuma don karbar baki.
Kayan hadi:
• Fulawa
• Butter
• Gishiri (kadan)
• Nama ko kaza
• Dankalin Turawa
• Attarugu da albasa
• Sunadarin dandano
• Curry da thyme
• Bakar hoda (Baking powder)
• Meat pie cutter
• Man gyada (in soyawa za a yi)
• Oven (in gasawa za a yi)
• Meat mincer
Yadda ake hadin:
Bayan uwargida ta yanka nama ko kaza, sai ta silala da sunadarin dandano da curry da thyme da albasa har sai naman ya yi laushi.
Sannan ta tsame ta zuba a meat mincer ta cakuda naman. Idan ba ta da meat mincer sai ta yayyanka naman kanana sannan ta jajjaga shi da attarugu.
Sai ta sa mai kadan a kan wuta kafin ta mayar da dakakken naman ta yayyanka dankalin Turawa, sai ta dafa shi, sai ta yanka shi kanana.
Sai ta hada da dakakken naman a wuta tana gaurayawa. Idan sun nuna tare sai ta sauke daga wuta.
Sai uwargida ta dauko fulawarta ta zuba butter kamar karamin cokali biyu da bakar hoda da gishiri kadan.
Sai ta yi ta kwabawa da dan ruwa kadan. Sai ta yi masa kwabin cincin. Sannan ta sa shi a tire filla-filla kamar za ta yanka cincin.
Sai ta dauki Meat Pie Cutter ta yanka. Sannan sai ta zuba kayan su naman da dankalin a tsakiyar Meat Pie Cutter sai ta ku ninke.
Ta soya ko kuma ta gasa shi a gas. Lallai sai kunnen maigida ya yi motsi.