Yadda ake hada shinkafa mai fasili

  Kayan hadi . Shinkafa . Ganyen Fasili . Man gyada . Tafarnuwa . Sinadarin dandano   Yadda ake yi Da farko uwargida za ta samu shinkafarta ta zuba mata ruwa ta dora a wuta, ta dafa ta. Amma kada ta dahu sosai, sai ta sauke ta wanke ta kuma tace ta bar ta a […]

Yadda ake hada shinkafa mai fasili

  Kayan hadi

. Shinkafa

. Ganyen Fasili

. Man gyada

. Tafarnuwa

. Sinadarin dandano

 

Yadda ake yi

Da farko uwargida za ta samu shinkafarta ta zuba mata ruwa ta dora a wuta, ta dafa ta. Amma kada ta dahu sosai, sai ta sauke ta wanke ta kuma tace ta bar ta a cikin matsami ta karasa tsanewa.

Daga nan sai ta samu wata tukunyar ta zuba man gyada a ciki, ta kawo tafarnuwa ta zuba, ta soya shi sama-sama. Sai ta dauko shinkafar nan da ta dafa ta zuba a ciki sai ta juya. Daga nan sai ta zuba sinadarin dandano.

Sai kuma ta dauko ganyen fasili mai yawa ta gyara ta yanka shi. Sai ta zuba a cikin shinkafar nan, sa’annan ta sa murfi ta rufe. Idan ta dahu sai a sauke a kwashe.

Ana cin wannan shinkafa da miyar nikakken nama.