Yadda ake hada ‘yogurt’ na gida (Home made Yogurt)
Madarar yogurt na daga cikin kayan sha masu lafiya da amfani a jikin dan Adam. Ana yin yogurt ne daga madara da sauran kayan hadi. Ana shan sa haka ba tare da an sa wani abu a ciki ba; za kuma iya shan sa da sukari ko ’ya’yan itatuwa da dai sauransu. Kayan hadi: Madara […]
Madarar yogurt na daga cikin kayan sha masu lafiya da amfani a jikin dan Adam. Ana yin yogurt ne daga madara da sauran kayan hadi.
Ana shan sa haka ba tare da an sa wani abu a ciki ba; za kuma iya shan sa da sukari ko ’ya’yan itatuwa da dai sauransu.
Kayan hadi:
- Madara kofi hudu
- Ruwa kofi hudu
- Sukari kofi
- Flavor mai kamshin madara cikin cokali.
- Corn starch kofi daya
- Culture rabin cokali
Yadda ake hadin:
Da farko za a kwaba madarar (ta gari) da sukari da corn starch sai a zuba ruwan sanyi a kai.
Daga nan sai a tafasa ruwan zafi a zuba a kai, idan an dan dade sai a juya shi har sai an tabbatar babu kulalai ko kadan a ciki.
A murje hadin ya zama ruwa sannan a bar shi ya huce ya zama da dumi.
Kafin ya yi sanyi sosai sai a zuba culture a ciki.
Bayan an sa culture sai a rufe a bari ya yi awa takwas zuwa 12, ko ma ya kwana.
Idan aka bude shi sai a zuba sukari da flavor sai a motsa.
Idan yogurt din ya hadu sai a sa a fridge a bar shi ya yi sanyi.
Daga nan sai a sha shi yadda ake so.
Karin haske:
Za a iya amfanin da madarar gari ko ta ruwa wajen hada yogurt na gida.
Idan da madarar gari za a yi amfani, to yadda na yi bayani haka za a yi.
Idan kuma da madarar ruwa ce, to a dafa madarar sa’annan a diga mata culture, a rufe na tsawon awa takwas koh sha biyu.
Wannan shi ne yadda ake yin yogurt a gida daki-daki.
Za ku kuma iya sha da fura ko a kankare kwakwa a ciki yogurt din a sha da shi.