Yadda ake hadin garin dilke don kawata fata

An fi sanin mutanen Borno da gyaran jiki. A cikin abubuwa da dama da suke amfani da su don gyara fata, a yau na kawo muku yadda ake hada dilke. Ana yin dilke ne ga amare kafin bikinsu. Akwai hanyoyi da dama da ake hada dilke; akwai na dankali da na gyada. Yin dilke a […]

Yadda ake hadin garin dilke don kawata fata

An fi sanin mutanen Borno da gyaran jiki. A cikin abubuwa da dama da suke amfani da su don gyara fata, a yau na kawo muku yadda ake hada dilke. Ana yin dilke ne ga amare kafin bikinsu. Akwai hanyoyi da dama da ake hada dilke; akwai na dankali da na gyada. Yin dilke a jiki na taimaka mana wajen cire fatar da ba ta da amfani a jikinmu kuma ta sa fata mai gausti ta yi santsi da laushi.

Abubuwan da za a bukata

  • Gyada
  • Man zaitun
  • Ruwa

 

Hadi

A nika danyar gyada tare da bawonta. Sannan sai a wanke da ruwa, a sa a matsami sannan sai a soya ta da mai kadan har sai ta canja launi ta koma ruwan kasa.

Yadda za a shafa

A tafasa ruwan zafi sannan sai a kwaba garin dilke da dan mai kadan har sai hadin ya yi kauri. Bayan haka, sai a jika fatar jiki da ruwan dumi kafin a fara shafawa da tafin hannu. Bayan an gama dirza dilke a fata an cire dattin fata, sai a wanke da ruwan dumi. A bar jiki ya bushe kafin a shafa man shafawa.