Yadda ake hadin halawa domin samun santsin fata

Ana yin hadin halawa ce domin samun sulbin fata ko kuma ga matan da suke fama da gashin jiki kamar a hannuwa da kafafu. Halawa ta samo asali ne daga mutanen Borno wannan na daya daga cikin al’adunsu na gyara amaryar gobe kafin a yi mata rufi. Amma yanzu zamani ya canja inda har wasu […]

Yadda ake hadin halawa domin samun santsin fata
Yadda ake hadin halawa domin samun santsin fata

Ana yin hadin halawa ce domin samun sulbin fata ko kuma ga matan da suke fama da gashin jiki kamar a hannuwa da kafafu. Halawa ta samo asali ne daga mutanen Borno wannan na daya daga cikin al’adunsu na gyara amaryar gobe kafin a yi mata rufi. Amma yanzu zamani ya canja inda har wasu kabilu ke amfani da shi ga amaren gobe ko don gyaran fata. Kowace mace akwai irin ababen da take hadawa wajen yin hadin nata halawar, sannan ni ma na kawo muku irin nawa yanayin hadin. A kasance wajen yin halawa kamar sau daya a wata domin samun fata mai santsi da laushi da kuma rabuwa da gashin fata.

Abubuwan da ake bukata

•        Cokula uku na sukari

•        Lemun tsami uku

•        Ruwa cokali daya.

Hadi

A zuba sukari a tukunya mai zafi, idan ya fara narkewa sai a zuba ruwan lemun tsami da ruwa kadan. A tabbatar cewa wutar ba mai yawa ba ce wadda aka dora halawar a kai, domin kada ta kone. A yi ta gaurayawa har na tsawon minti 45 har sai hadin ya koma ruwan kasa. Sannan a sauke daga kan wuta a jira ya huce. Za a ga ya yi danko. Sai a samu cokalin katako ko na roba a shafa a kan fata inda ke da gashi. Bayan ya bushe, sai a samu tsumma a danna a kan fata sai a rika ciro shi. Yin hakan na fitar da gashin fata kuma za a ga fatar ta yi sulbi da santsi.