Yadda ake jan ra’ayin masu shiga tasi da rakiyar Mai dalilin aure

Ranar Larabar  makon jiya ne masu daukar shatar tasi a kasar Pakistan suka tashi da jin tallar neman fasinjoji, inda aka nuna musu garabasar kewaya gari tare da rakiyar Gwaggo Mai dalili, wanda a harshen kasar ake yi wa lkakabi da “Rishta.” Kamfanin Careem da ke mu’amala da abokan hulda ta wayar hannu o kafar […]

Yadda ake jan ra’ayin masu shiga tasi da rakiyar Mai dalilin aure

Ranar Larabar  makon jiya ne masu daukar shatar tasi a kasar Pakistan suka tashi da jin tallar neman fasinjoji, inda aka nuna musu garabasar kewaya gari tare da rakiyar Gwaggo Mai dalili, wanda a harshen kasar ake yi wa lkakabi da “Rishta.” Kamfanin Careem da ke mu’amala da abokan hulda ta wayar hannu o kafar sadarwar intanet ne ya fito da wannan sabon salon talla.

Gwaggon rishta dai mai hada aure ce da ta shahara a kasashen Kudancin asiya, kuma tana tattara muhimman bayanai game da mata da maza da ke son yin aure, al’amuran da suka hada da matakin iliminsu da albashinsu da tsawonsu, har ma launoin fatar. Bayanan dai ke bat a damar samun dacen hada mutane su zama ma’aurata.

Irin wadannan mata ana ganinsu sanye da gwaureren tabarau dauke da kundin  sunaye da tsohuwar wayar nokia. Irin wadannan mata dai kamfanin sufuri na Careem na bijiro da kimar bayanan da suke tare  das hi.

Shiga tasi tare da Gwaggo Rishta an bullo da tsarin ne a biranen  kasar Pakistan biyu, al’amarin da ya dauki hankalin masu aikewa da sakonnin twitter, inda suka rika yabo da suka.

“Tsarin Careem halattace ne, sai dai yanzu mutum zai kasance tare da Gwsago Rishta wadda za ta kewaya da shi,” a cewar barkwanci mai amfan I da shafin tweeter, Faraz Ahmed (@CrazeeGentlemen), wanda ya baza reanbar 19 ga Yuli 2017.

Sai dai wasu sun dauka yaudara ce kawai wajen dabarun tallata wa fasinjoji shiga tasi din kamafani.

“Hawa mota tare da Gwaggo Rishta nasara ce ga @CreemAK, al’amarin da tun karfe 1 da 33 masu tallata haja ke ta magana a kai,” inji Amnaa Tarik kamar yadda ya aike a sakons ana tweeter.

“Ta yiwu a lokacin da aka tuka motar mutane na iya bijiro wa gwaggo da bukatarsu, ta yadda za ta kulla musu alakar da ta dace da su,” inji Nakbiu

Kamfanin sufuri na Careem Pakistan ya yi hanzari kare manufarsa da cewa halattaciya ce.

“Mun fahimci cewa matasn da ke aikin Rishta sun shahara a tattaunawar man uyan mutane. Don haka muka kaddamar da shirin don taimaka wa matasa su samu abokan zama da suka dace da su,” a cewar shugaban sashen hulda da jama’a na Careem Pakistan, Sibtain Nakbi, kamar yaddda kafafen yada labaran kasar suka bayyana.Wannan ba shi ba ne karo na farko da kamfani tasi ke bullo da sabuwar dabarar tallata haja. A cikin Janairun bana, kamafani ya bullo da kewaya a cikin motarsu tare da likita, wato abin da aka Turance aka yi w alakabi da “Careem Doctor,” da manufar kawo wa abokin hulda kwararren mai kula da lafiya ko likita kusa da shi.

Matashi ya kashe mahaifinsa kan N5,000 a Delta

Muhimman batutuwa da Biden ya taɓo a jawabin yi wa Amurkawa bankwana

IPMAN ta musanta batun ƙara farashin man fetur

Gwamnatin Tinubu ta yi wa Sarki Sanusi raddi