Yadda ake jus ɗin karas da lemon zaƙi
A yau na kawo muku yadda ake jus ɗin karas da lemon zaƙi domin shan ruwa.
Assalamu alaikum Uwargida. Barkanmu da ci gaba da gudanar da ibadar watan Ramadan tare da fatan ana cikin koshin lafiya.
Yanzu lokaci ya yi da za a samu takarda da alkalami domin rubuta irin girkin da za a yi a wannan wata mai alfarma.
Sannan kada a sha’afa da girke-girke a daina ibada.
A yau na kawo muku yadda ake jus ɗin karas da lemon zaƙi domin shan ruwa. Tare da fatan za a gwada domin jin daɗin maigida da sauran mutanen gida.
Abubuwan da za a bukata
· Karas
· Lemon zaki
· Sukari
· Filebo
· Kankara
Haɗin
A kankare karas a wanke, a kuma yayyanka kanana a ajiye a gefe.
A wanke lemon zaƙi sannan a bare shi a cire kwallon a zuba a na’ura bilenda a markade shi.
Sai a zuba su baki ɗaya a ciki tare da kankara wacce aka dan farfasa ta. Sannan a markada har sai sun yi laushi.
Sai a sa rariyar tata a tace kamar sau biyu. Sannan a dauko sukari a zuba da filebo mai dandanon lemo.
Sai a yi ta gaurayawa har sai sukarin ya narke, sannan a dauko tsaftataccen mazubi a zuba a ciki sannan a sa a gidan sanyi.
Bayan an ci abu mai dumi ne ya kamata a sha wannan hadin, domin yin buda baki da abu mai sanyi sosai na haifar da matsalar lafiya. Don haka sai a kula.