Yadda ake juyayin rasuwar Sarkin Zazzau

A ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 ne Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau, Marigayi Alhaji Shehu Idris rasuwa bayan fama da rashin lafiya. Ga wasu daga hotunan yadda aka dauki gawar basaraken daga Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna har zuwa isarta Zariya, inda za a yi mata sallah da misalin karfe biyar […]

Yadda ake juyayin rasuwar Sarkin Zazzau

A ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 ne Allah Ya yi wa Sarkin Zazzau, Marigayi Alhaji Shehu Idris rasuwa bayan fama da rashin lafiya.

Ga wasu daga hotunan yadda aka dauki gawar basaraken daga Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna har zuwa isarta Zariya, inda za a yi mata sallah da misalin karfe biyar na yamma.

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero na daga cikin sarakunan da suka fara isa Fadar Sarkin Zazzau domin ta’aziya gabanin jana’iza.
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari yayin mika ta’aziya a Fadar Sarkin Zazzau
Sarkin Kazaure Najib Hussaini Adamu gabanin sallar jana’izar Sarkin Zazzau a Zariya
Jama’a sun yi ta taruruwa zuwa Fadar Sarkin Zazzau domin mika ta’aziya bayan samun labarin rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.
Wasu daga cikin masu jiran isowar gawar basaraken a Zariya bayan samun labarin rasuwarsa.
Yada daga cikin motocin da suka rako gawar Sarkin Zazzau daga Kaduna zuwa Zariya
Jama’a a Fadar Sarkin Zazzau na nuna kaduwa da samun labarin rasuwar sa.
Taron jama’a sun tarbi gawar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris a fadarsa.
Lokacin da ake shirin daukar gawar sarkin daga asibitin sojoji na 44, Kaduna zuwa Zariya
Jami’an Fadar Sarkin Zazzau a Babban Asibitin Sojoji na 44, Kaduna, inda Allah Ya yi wa Sarki Shehu Idris rasuwa.
Kofar Fadar Sarkin Zazzau, inda mutane ke ta zuwa domin nuna alhini game da rasuwar.