Yadda ake kasuwanci a yanayin zafi a Sakkwato
Bashar Salisu dan shekara 26 da ya kwashe shekara uku yana sayar da kayan sanyi kama daga ruwan leda da na roba da lemun kwalba, ya ce kasuwanci a yanayin zafi yana tattare da kalubale musamman saboda rashin wutar lantarki da karin kudin haraji daga gwamnati da hauhawar kudin sufuri. Bashar ya ce, “In yanayin […]
Bashar Salisu dan shekara 26 da ya kwashe shekara uku yana sayar da kayan sanyi kama daga ruwan leda da na roba da lemun kwalba, ya ce kasuwanci a yanayin zafi yana tattare da kalubale musamman saboda rashin wutar lantarki da karin kudin haraji daga gwamnati da hauhawar kudin sufuri.
Bashar ya ce, “In yanayin zafi ya soma, cinikinmu yakan karu sabanin lokacin sanyi don in kana sayar da katan biyar na ruwa ko lemu a lokacin sanyi, yanzu 15 za ka sayar saboda ana nema. Sai dai cinikin namu na tattare da kalubale saboda masu wutar lantarki sun kara mana kudi wai muna shan wuta da yawa duk da babu wutar. Masu karbar haraji ma ba su bari mu huta wai saboda yanzu lokacinmu ne. Haka tunda yawan kayan da kake daukowa ya karu nan ma dole kudin sufurin ya daga.”
“Duk da wannan kalubale ana samu domin idan ka sayo katan 10 za ka sayar da 9, shi ne ya sanya kake ganin kayan suna katsewa domin yakan kai babu a kamfani, su kuma ’yan kasuwa sun boye kayan don kada su cika kasuwa bukatar ta rage, ka ga a haka in sun kara farashi ba za a saya ba, amma in ka zo kana bukata babu ko nawa aka ce za ka saya, duk wani abu da ake sha a wannan yanayi sun kara kudi,” inji shi.
Bashar ya ce ya je Kamfanin Pepsi sayen lemu aka ce masa babu, ya tambaya me ya sa haka, sai suka fada masa suna da wani tsari kowace rana akwai irin lemun da za su yi sabanin wani yanayi da ba wannan ba da suke yin duk nau’o’in lemunsu a lokaci daya, saboda yanzu bukata ta fi yawa.
Ya ce a shagonsa da ke kan Titin Abdullahi Fodiyo huldarsa da mutane yanzu sai da hakuri don bukata ta karu, saboda yanayin zafi kasuwarsu na budewa suna samu daidai gwargwado.
Alhaji Bello Jariri mai kasuwancin fanka shekara kusan 20 ya ce suna cinikin fanka sosai duk da ta kara kudi, domi fankar da za a sayar dubu 18 a baya yanzu sai dubu 22 ne za a samu, hakan na karuwa ne saboda karin da aka samu ga kamfani, sai kuma gwamnati da ta kara haraji.
Ya ce duk wani mai harkar ba ya zaman kashe wando a wannan yanayi domin kullum yana iya sayar da fanka 10.
“Fanka mai caji da wadda ba a yi mata caji suna shiga sosai a wannan lokaci. Yanzu za ka same mu kullum cikin aikin hada fanka don masu saye suna jirarmu, da ka hada za su dauka, ciniki na tafiya sosai a wannan yanayi sai godiyar Allah,” inji Jariri.