Yadda ake kasuwancin kodar mutane a Abuja

Abokan wani matashi sun sace kudin da aka ba shi bayan ya sayar da kodarsa

Yadda ake kasuwancin kodar mutane a Abuja

A wani binciken kwakaf na tsawon wata uku da Jaridar Aminiya ta gudanar, ta banƙado yadda ake kasuwancin ƙoda a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Bincike ya gano yadda aka baza matasan garuruwan da ke kewaye da Babban Birnin Tarayya don jawo hankalin samari masu karamin ƙarfi su sayar da ƙodarsu.

Ƙaruwar sayar da ƙoda ya jaddada buƙatar Ƙungiyar Likitocin Nijeriya da Hukumar Ba da Lasisin Likitanci da ma Ma’aikatar Lafiya su ɗauki mataki a kan asibitocin da ke wannan harƙallar ta dashen ƙoda, ba bisa ƙa’ida

Mararraba wuri ne da ya ƙunshi dubban samari majiya ƙarfi waɗanda akasarinsu masu ƙaramin karfi ne da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Mararraba dai na ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa, inda ake yin kowane irin kasuwanci, ciki har da kasuwancin ƙodar mutum.

A Tudun Wada da ke Unguwar Mararaba ce wani mai suna Aminu Yahuza ya yi tunanin kashe kansa a watan Yunin 2023.

Aminu matashi ne mai shekara 25 da ke fama da talauci.

Domin rage raɗaɗin da yake ciki, sai ya tuntuɓi wani ƙaninsa mai suna Abbas Yusuf ƙan shekara 23 domin ya haɗa shi da waɗanda ke yi wa mutum hanyar sayar da ƙodarsa.

Bayan ya sayar da ƙodarsa ga wata mata mara lafiya ’yar ƙasar “Afirka ta Kudu” a watan Yunin 2022, sai Abbas ya yi maza, ya kira abokinsa Abdulrahman, wanda ke irin wannan aikin nemo masu son su sayar da ƙodarsu cewa, akwai wani wanda zai sayar da ƙodarsa .

Ba tare da ɓata lokaci ba, sai aka ɗauki samfurin jinin Aminu, inda bayan ’yan kwanaki, aka cire masa ƙodar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja, inda aka dasa wa wani majiyyaci.

Da yake farashin ƙodar Naira miliyan 1 ne, sai aka damƙa masa wannan kuɗi, lamarin da ya sa shi cikin farin ciki, amma daga bisani wasu abokansa biyu suka ha’ince shi, suka sace rabin kuxin.

“Na rasa ƙodata, ba ni da kuɗi ko aiki, kuma ba ni da ƙarfin yin wani aiki mai wahala,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

Shi kuwa ɗan uwan Aminu wato Abbas ya sayar da qodarsa a kan Naira miliyan 1.2 a bara, wanda shi ne farashi mafi tsoka da aka taɓa sayar da ƙoda.

Shi ma Abbas wasu abokansa guda biyu, wato Abdulrahman da Habib ne suka ruɗe shi ya sayar da ƙodarsa.

Su kuma waɗannan mutum biyun suna cikin masu nemo waɗanda sayar da ƙodarsu, ƙarƙashin wani babban mutumin da ke kasuwancin sayar da ƙoda a Legas.

Aikinsu shi ne nemo matasa maza da mata da suke fama da talauci su yaudare su, har su amince su sayar da ƙodarsu.

Aminiya ta gano cewa, ƙalubalen matsanancin tattalin arzikin Nijeriya na ɗaya daga cikin abubuwan da ke ingiza matasa da dama sayar da ƙodarsu a kan farashin da bai wuce Naira miliyan 1 ba.

Ana zargin Asibitin Alliance da ke Garki Abuja da cire ƙodar aƙalla ƙananan yara uku.

A watan Agustan 2023, Aminiya ta rwauito yadda wani bakanike ɗan shekara 16 mai suna Oluwatobi Adedoyin da ke Masaka a Ƙaramar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa ya sa abokinsa mai suna Yellow ya sayar da ƙodarsa a kan Naira Miliyan 1 kuma aka raba kuɗin gida uku bayan an tilasta masa barin Abuja.

Tun daga wannan lokacin, labarin cinikin ƙoda ya bazu a garin, kuma aka samu wa5xanda abin ya shafa da suka fito don ba da labarin yadda suka sayar da ƙodarsu.

A ƙa’ida, ba da gudummawar ƙoda ra’ayi ne na ƙashin kai don taimako, musamman ma idan aka yi la’akari da sanarwar yajejeniyar da aka yi a Istanbul a 2008 game da fataucin gaɓoɓin jiki da yawon buɗe ido, wadda ta yi kira da a haramta kasuwancin gaɓoɓin jikin ɗan Adam ko wani sashe na jikinsa.

A ƙasar Iran haramun ne saya da sayar da gaɓoɓin jikin ɗan Adam, musamman idan ma’aikatan lafiya ko cibiyoyin kiwon lafiya suka yi haɗin baki da masu buƙata don a nemo wasu masu ƙaramin ƙarfi ko ƙananan yara ko kuma mutanen da ba su da ƙarfin tattalin arziki.

Duk da haka, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, ana harƙallar kasuwancin ƙoda fiye da ɗaya a kasuwar bayan fage a kowace sa’a.

Cinikin ƙodar ƙananan yara

Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a watan Nuwamban 2022, an ga bidiyon wani matashi da ake zargin asibitin Alliance da ke Abuja ya cire ƙodar ƙaninsa mai shekara 17 da haihuwa.

A cikin bidiyon, matashin ya zargi asibitin da rashin sanin makamar aiki kafin a yi masa tiyata.

Mahukuntan asibitin dai a wata ganawa da manema labarai sun musanta zargin, inda suka ce ‘mai bayar da ƙodar ya sanya hannu kan takardar amincewa tare da gabatar da takardar shaidar da kotu ta nuna cewa shekarunsa sun haura 18.

A watan Fabrairun 2023, sai asibitin ya sake cire ƙodar wani mai suna Oluwatobi Adedoyin, wanda ƙaramin yaro ne.

Hakazalika, a watan Yunin 2023 ya sake cire ƙodar wani mai suna Yahaya Musa, mai shekara 16 duk da irin fallasar da bidiyon na Nuwamba 2022 ya yi.

Daraktan Kula da Lafiya na asibitin, Dokta Christopher Otabor ya dage a kan cewa asibitin kawai yana tabbatar da masu ba da gudummawar ƙodar sun cancanta kuma sun dace da marasa lafiyar da za su ba wa ƙodarsu don a dasa musu.

A watan Agusta, Dokta Otabor ya shaida wa wannan jarida cewa asibitin yana bin doka, inda ya ce, sai masu ba da gudummawa sun gabatar da takardun shaida tare da sanya hannu kan takardar amincewa kafin tiyata.

Kamar Oluwatobi wanda ƙodarsa aka cire aka dasa wa wani Egbuson Sampson, wanda asibitin ya ce yanzu ya rasu, Yahaya Musa yana ƙarami ne a lokacin da aka lallaɓe shi ya sayar da ƙodarsa a kan Naira milyan 1.

Takardar shaidar Ma’aikatar Lafiya ta Bauchi ta nuna cewa an haife shi ne a ranar 9 ga watan Satumba, 2007 a Jihar Bauchi.

Da yake ba da labarin yadda wani ya shawo kansa ya sayar da ƙodarsa, matashin mai shekara 16 ya ce, “Ya shaida min cewa akwai asibitin da ke sayan ƙoda kuma ya sayar da tasa a kan Naira miliyan 1.”

Bayan an duba jininsa, an cire ƙodar Yahaya, inda washegari aka sallame shi daga Asibitin Alliance, inda ya biya wa wanda ya yi masa hanya kashi 10 na kuɗin.

Katin magani da aka rubuto masa don kula da lafiyarsa bayan tiyatar da wannan jarida ta samu na ɗauke sa-hannun Dokta Aremu Abayomi Adeniran, babban likitan da ke kula mata da kuma mataimakin Darakta Kula da Ayyukan Asibitin Alliance. Likitan ya yi wa Oluwatobi tiyata a watan Fabrairun 2023.

Da yake bayyana irin raɗaɗin da yake fama da shi a yanzu, Yahaya ya ce, “Asibitin ya ba ni wasu magunguna bayan an yi min tiyata, amma na koma na ce musu magungunan sun ƙare, amma kuma ina ci gaba da jin zafi a cikina.

“Dokta Aremu ya ce in sha Paracetamol duk lokacin da na ji zafi.” Bayan wata biyar da cire qodar, Yahaya ya ce cikinsa bai daina ciwo ba.

Mahaifin Yahaya, wato Musa Yahaya ya tabbatar da faruwar wannan lamari, sai ya kai rahoto ofishin ’yan sanda na Garki, inda aka sanar da ’yan sandan su kuma suka gayyaci Dokta Adeniran domin ya amsa tambayoyi, amma daga baya suka sallame shi.

Yadda dillalan ƙoda ke cin karensu babu babbaka

Binciken da wannan jarida ta yi ya nuna cewa, wani dillalin sayar da ƙoda da ke zaune a Legas da ke aiki da Kamfanin Pseudonym da ake kira Mayor ya ɗauki samari maza aiki a matsayin wakilansa domin su jawo yara maza irin su Oluwatobi da Yahaya su sayar da ƙodarsu ga masu ciwon ƙoda.

Masana sun ce, sama da ’yan Nijeriya miliyan 20 ne ke da mataki ɗaya na matsanancin ciwon ƙoda ko kuma wani mataki na daban.

Wani mai ba da shawara kan ciwon ƙoda a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Farfesa Aliyu Abdu, ya yi ƙiyasin kusan kashi biyar cikin 100 na duk waɗanda ke da matakai daban-daban na cutar suna da mataki na biyar, wato matakin CKD da ake iya dashen qoda.

Ya bayyana cewa yawancin marasa lafiya da ke fama da cutar ƙoda suna zuwa asibiti ne a makare.

Sakamakon ba a yarda a cire ƙodar mamaci a Nijeriya da kuma rashin tsari wajen dashen ƙodar ke sa da yawa ke neman ƙodar ta bayan fage.

Aminiya ta gano cewa, suna haɗa kai da dillalan ƙodar da ke ɗaukar ma’aikata irin su Yellow a Masaka da Abdulrahman da Habib a Mararaba domin nemo matasa masu ƙaramin ƙarfi da ke da buƙatar kuɗi.

Wannan jarida ta tabbatar da samun bayanai daga wajen samari shida a Mararaba da Masaka, inda ta yi magana da huɗu daga cikinsu, da shekarunsu ba su wuce 25 ba, waɗanda ke da tabo da ke nuna cewa an cire musu ƙoda.

Yawancin wakilan da ke nemo masu sayar da ƙodarsu su ma sun sai da tasu kamar Yellow da Abdulrahman da Habib.

Haka kuma dukkansu sun ce sun yi aiki da wannan babban dillalin da ke Legas wanda ya gabatar da kansa ga Oluwatobi, a matsayin ma’aikacin Asibitin Alliance.

Sai dai asibitin ya musanta hakan.

Amma yaran nan biyu, wato Yahaya da Oluwatobi sun ce dillalin ya saba da yawancin ma’aikatan asibitin.

Musa Yahaya ya ce, “A fahimtata, duk lokacin da wasu asibitocin Abuja ke buƙatar ƙoda za su kira wakilansu da ke samo musu waɗanda za a sayar da ƙodarsu, mutumin zai kira Habib ko Abdulrahman ya ba su bayanin irin jinin mai ƙodar da ake buƙata.

Idan Abdulrahman ya samu ‘mai bayarwa’ za su yi ciniki da kasonsa, sannan ya gayyace shi domin a gwada jininsa. Idan ya yi daidai da wanda ke buƙata shi ke nan.’

Abbas Yusuf ya ce, “Idan duk wanda ke son sayar da ƙodarsa zai kira wakilansa, shi kuma wakilin zai kira wannan mutumin na Legas ko wasu manyan dillalai irinsa su shirya.

“Idan mutum ya je sai ya dawo da Naira miliyan 1, inda zai ba wa wakilin da ya kai shi Naira 100,000’’.

A binciken wata uku da Aminiya ta gudanar ya kai ta ga gano sabuwar lambar wayar da mutumin nan na Legas ke amfani da ita, wadda manhajar tantance sunayen da aka yi rijistar lambar waya wato ‘Truecaller’ ta bayyana sunansa da Emmanuel Olorunishola.

An ce ya yi watsi da tsohuwar lambar wayarsa, wadda ya yi rajista da sunan Mayo Pseunonym, ya gudu zuwa Legas.

Tona asirin kasuwancin ƙoda na Abuja

Sakamakon yawaitar cutar ƙoda, buƙatun ƙodar na ƙaruwa a duk faɗin duniya, inda ƙasashe masu tasowa ciki har da Nijeriya ke zama kan gaba wajen sayar da ƙodar ga masu buƙatar ta hanyar da ba ta dace ba.

Aƙalla an yi dashen ƙoda guda 1,353 a Nijeriya daga 2005 zuwa yau, kamar yadda ƙungiyar da ke sa-ido kan ba da gudummawar ƙoda da kuma dasawa ta duniya ta bayyana.

Nijeriya ba ta da wata hukuma da ke ba da lasisin cibiyoyi masu dashen ƙoda saboda kowace cibiya tana bin ƙa’idojin likitanci ne.

Wannan ya haifar da wani giɓi da ke ƙarfafa haramtacciyar hanyar yin fataucin sassan jikin ɗan Adam.

Wata majiya da ke da masaniyar ‘kasuwancin’ ta shaida wa Aminiya cewa, wani dillalin ƙoda da ke aiki a ɓoye yana tattauna farashin da majinyatan da ke fama da ciwon ƙoda.

Wasu daga cikin majinyatan ’yan ƙasashen waje ne, don haka za su iya biyan kusan Naira miliyan 5 ga dillalin.

Dillalin shi kuma zai saya Naira miliyan 1.

Wakilin yana samun kashi 10 na miliyan 1 da kuma wani kashi 10 daga dillali. Ka ga zai tashi da Naira dubu 200 ke nan.”

Wata majiya ta bayyana cewa, saboda yawancin asibitoci masu zaman kansu na karɓar kuɗi daga Naira miliyan 10 zuwa Naira miliyan 15 don aikin dashen ƙoda, inda suke buƙatar dillalai don samun gwaggwaɓar riba.

“A 2022 ƙanwata ta buƙaci a yi mata dashen ƙoda kuma asibitin da ke kula da ita mai zaman kansa ne a Abuja, wanda ya shaida mana cewa, za su iya taimaka mana wajen samo mata ƙodar.

“Sai dai ɗan ’yar uwata ya ba da ƙodarsa kuma duk da haka ta rasu bayan wasu watanni,” in ji wani mazaunin Abuja da ya nemi a sakaya sunansa.

Kodayake Abbas da Aminu da Oluwatobi da Yahaya sun samu nutsuwa aikin tiyatar saboda likitoci da suka gudanar da aikin a asibitoci masu zaman kansu masu lasisi ne.

Sai dai wani ƙwararren likita, Farfesa Aliyu Abdu ya yi gargaɗin cewa, akwai illa ga lafiya a nan gaba, idan aka yi dashen ba bisa ƙa’ida ba.

Yadda muka yi shigar burtu a matsayin dillalan ƙoda

A ƙoƙarinmu na tantance sahihancin bayanan da muka samu, Aminiya ta yi sigar burtu, inda aka haɗa mu da wani dillalin ƙoda mai suna Chiboy, amma mun tabbatar sunansa Joseph Paul Chimobi, wanda ya ce shekarunsa 18 kuma yana zaune a Mararraba.

Haka kuma shi ma an ce yaron babban dillali nan ne na Legas da ake kira Mayor.

Da farko ya yi ɗar-ɗar, inda ya nemi sanin ta yaya wakiliyarmu ta samu lambarsa, sai ta ce masa daga wurin ma’aikacin kiwon lafiya a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja, sannan hankalinsa ya kwanta, inda ya buƙaci a tura masa kuɗin mota ta asusunsa na Palmpay.

Ya ce yanzu farashin ƙoda ya kai Naira miliya biyu, wanda ya ce yanzu yaran ba sa yarda a kan Naira miliyan 1.

Bayan an yi ciniki sai aka daidaita a kan za a ba shi Naira miliyan 1.5, sannan ya tunatar da wakiliyarmu cewa, kuɗin aikinsa kaso goma ne na kuɗin, wato Naira 150,000.

Washegari sai Chiboy ya sake roƙon a ba shi ƙarin Naira 5000, saboda a faɗarsa wanda zai ba da ƙodar tasa yana Keffi ne, sai wakilyarmu ta ce su daure su ƙaraso Abuja za a biya su kuɗin da suka kashe.

Da misalin qarfe 12:30 ranar wata Talata, sai Chiboy ya zo da wanda zai ba da ƙodarsa mai shekara 38 suka haɗu a wani wuri a Abuja.

Lokacin da ake tattaunawa, Chiboy ya yi shiru ya bar wakiliyarmu da mutumin su daidaita.

Sai dai shi wanda zai ba da ƙodar da ke da mata da ’ya’ya biyu ya ce, yana ɗan shan giya kaɗan. Wannan shi ne ya sa wakiliyarmu ta nemi ragin kuɗin qodar, kuma ta bayyana cewa za ta shaida wa wanda ke bukatar.

Shi dai wannan mutum da yake aiki a wani otel ya kafe a kan cewa zai kula da iyalinsa ne domin an kore shi daga aiki, kuma ita ma wakiliyarmu ta dage ta ce za ta sanar da wanda za a yi wa aikin ƙodar. Sai Chiboy ya tsoma bakinsa, inda nan take ya ba Asibitin Alliance da shawarar a yi amfani da Asibitin Alliance domin yin tiyatar.

Da aka tambaye shi dalili, sai ya ce, “Alliance suna yi da sauri, kuma a can nake aiki a da.”

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya bar Alliance, sai ya ce: “Mayor wato wannan dillalin baya yin aikin yanzu. Yana da lokacin da yakan zo ya yi wani abu kamar haka.

“Amma yanzu bai cika zuwa ba, yanzu a Legas yake yana aikin kamfani.”

Mai ba da ƙodar ya yi baƙin ciki kuma ya ce ya fahimci abin da ya yi, amma yana buƙatar yin hakan domin kula da ’ya’yansa.

A yayin tattaunawar, Chiboy ya tabbatar da cewa, mutumin Legas wato Mayor yana taya kowace ƙoda tsakanin Naira miliyan 1 zuwa miliyan 1.3.

Ya dage kan cewa farashinsa a matsayinsa na wakili zai kasance kaso, inda ya ce Mayor na Legas na biyan sa Naira dubu 250,000 a kan duk mutum ɗaya.

Bayan mun tattauna tsawon sa’a ɗaya, sai muka yi bankwana kuma wakiliyar tamu ta tabbatar wa Chiboy da wanda zai ba da ƙodarsa cewa za ta tuntuɓe su bayan ta yi magana da majiyyacin.

Chiboy ya samo ƙarin masu ba da ƙoda

Kwana guda bayan ganawa da Chiboy da mai ba da ƙodarsa, Aminiya ta sanar da Chiboy cewa majinyacin da ke son ƙoda ya ce zai bayar da Naira miliyan 1 saboda mai ƙodar bai cika ƙa’idodin da ake buƙata ba.

Sai mai ba da qodar ya ce an yi masa tayin Naira miliyan 2 na ƙodarsa a Minna, Jihar Neja, amma ba ya son tafiya Minna, amma Aminiya ta dage a kan hakan.

Duk da an faɗa masa majinyacin ya samu wata qodar, Chiboy ya ci gaba da kira ko akwai buƙatar hidimarsa.

Hukumar NAPTIP ta damƙe Mayor bayan rahoton Aminiya

Makonni kayan bayan ganawa da Chiboy da mai ba da ƙoda, Aminiya ta samu bayanin cewa Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Ƙasa (NAPTIP) ta kama Mayor.

Kamen dai ya biyo bayan tattaunawa da Aminiya ta yi da jami’an hukumar ta NAPTIP.

Wani babban jami’in hukumar ya tabbatar da cewa, Hukumar NAPTIP na ci gaba da gina matakan fara shari’a da mutumin da abokanansa

Akwai sakacin Ma’aikatar Lafiya wajen sayar da ƙoda

Cirewa da dashen gaɓoɓin jikin ɗan Adam yana ƙunshe ne a cikin Dokar Kiwon Lafiya ta Nijeriya ta 2014, sashe na 54 (3) (a) da (b) na dokar cewa, Kwamitin Manyan Asibitoci na Ƙasa ne za su tsara sharuɗɗan amincewa da wuraren dashen gaɓoɓin da kuma ma hanyoyin da za a bi.

Aminiya ta ruwaito cewa, ba a yin hakan.

Tsohon Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire ne ya ƙaddamar da Kwamitin Tsare-tsare na Cibiyoyin Kiwon Lafiya na ƙasa a 2021 na tsawon shekara hufu kuma Farfesa Abiodun Phillips ne ke jagoranta.

Sai dai wata majiya daga ma’aikatar ta shaida wa Aminiya cewa, kwamitin bai yi aiki ba tsakanin 2021 zuwa Oktoba 2023.

Farfesa Abiodun Phillips ya shaida wa Aminiya ta wayar tarho cewa, gwamnati mai ci yanzu ta sake ƙaddamar da kwamitin a watan Nuwamba.

Ya ce za su yi aiki don sauya yanayin tsarin kula da lafiya na manyan cibiyoyin kula da lafiya na ƙasar nan.

Aminiya ta kai ga Ma’aikatar Lafiya domin samun kwafin ka’idojin amincewa da dashen gaɓoɓin jikin ɗan Adam da matakan da za a bi don amincewa da hakan da adadin cibiyoyin kiwon lafiya da suka cika waɗannan sharuɗɗan da kuma sunayensu da wuraren da suka dace.

Sai dai daraktar yaɗa labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar, Patricia Deworitshe ta roƙi Aminiya da ta gabatar da buƙatar a rubuce.

An miƙa buƙatar ’yancin yada labarai a ofishin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Ali Pate a ranar 5 ga Satumba, 2023.

Sai dai babu wani bayani daga ma’aikatar duk da cewa an kwashe makonni ana bin diddigin lamarin.

Wakiliyarmu ta bibiyi wasiƙar zuwa sashin Asibitin Koyarwa na Ma’aikatar kuma ta ziyarci sashin har sau biyu, amma daraktan ya yi alƙawarin ba da amsar wasiƙar. Duk da haka, har lokacin da ake buga wannan labari, ba a samu amsa ba.

Farfesa Abdu ya ce, “Akwai ƙa’idoji da aka gindaya na ƙasa da ƙasa da kuma na cikin gida ga masu gudanar da aikin dashen sassan jiki.

“Muna da na WHO waɗanda da sanannu ne, wato sanarwar Istanbul, wanda ya tara mutane a ƙarƙashin Hukumar Kula da Lafiya ta Majalsar Ɗinkin Duniya (WHO).

An wakilci ƙasashe daban-daban, ciki har da Nijeriya kuma sun samar da wani tsari da zai tabbatar da yadda za a riqa yin dashen ƙoda da sauran gaɓoɓi a duk fadin duniya.

Za mu kama masu harƙallar —Ministan Lafiya

Da yake mayar da martani kan binciken Aminiya, Ministan Lafiya, Ali Pate ya nuna damuwarsa kan lamarin.

Ali Pate ya ce, binciken na Aminiya ya nuna “yadda harƙallar ta yi kamari. Mun shiga alhini matuƙa bisa halin da waɗanda aka cutar suka shiga.”

Ya qara da cewa, “Lallai akwai ƙa’idojin kula da harkokin kiwon lafiya a Nijeriya, ciki har da dashen sassan jikin ɗan Adam kamar yadda yake a dokar NHA (2014).

“Sashe na 51-565 ya haramta wannan harƙallar da wannan jarida ta banƙado,” inji shi.

Pate ya ce, abu mafi muhimmanci a gare su shi ne tabbatar da bin waɗannan ƙa’idojin domin daƙile irin waɗannan harƙallolin, waɗanda a cewarsa daidai suke da duk wata harƙallar bayan fage.

Sai dai ya ce, kula da harkokin asibitoci yana kan gwamnatocin jihohi, inda ya ƙara da cewa, “za mu kafa kwamiti domin tabbatar da asibitocinmu kamar yadda wannan jaridar ta gano, ana bibiyar harkokinsu.

“Muna yaba yadda ’yan jarida suke gudanar da aikinsu.”

Waɗanda abin ya shafa sun kai ƙarar Asibitin Alliance suna neman diyyar miliyan 700

Waɗanda abin ya shafa sun kai karar Asibitin Alliance, inda suka buƙaci kotu ta karɓar musu diyyar Naira miliyan 700 daga asibitin.

Mai shari’a Abdullahi Aminu a ranar Litinin da ta gabata ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 19 ga Fabrairun 2024 domin ba wa asibitin damar shirya kare kansa.

Mahaifin ɗaya daga cikin waɗanda ake cire wa ƙoda mai shekara 16, Salaudeen Saliman, mai suna Adedoyin ne ya kai ƙarar Dokta Aremu Abayomi Adeniran da Dokta Christopher Otabor da Asibitin Alliance.

Bi-ta-da-ƙulli kawai ake yi mana —Asibitin Alliance

Da suke mayar da martani, hukumomin Asibitin Alliance sun bayyana cewa bi-ta-da-ƙulli ake yi musu.

Babban Likitan Asibitin, Dokta Otabor C.U. Fwa ya bayyana hakan a wata sanarda suka fitar cewa, “Wanda ya rubuta labarin ya ɗauki ɓangare, ya yanke hukunci, sannan ya buƙaci a yi hukunci ba tare da bin diddigi ba.

“Ina kira ga Jaridar Daily Trust ta ƙara bin diddigin lamarin, domin Asibitin Alliance ba shi da hannu a cikin harƙallar nan.

“Mun umarci lauyoyinmu su buƙaci jaridar ta janye wannan rahoto ko kuma mu kai ta ƙara kotu.”

Sai dai Babban Editan Jaridar, Malam Naziru Mikail ya ƙaryata batun asibitin, inda ya ƙara da cewa, “Labarin ya biyo bayan dogon bincike ne da ya ɗauki watanni. Don haka muna nan a kan bakarmu game da labarin,” inji shi.

An gudanar da wannan bincike tare da tallafin Gidauniyar Daily Trust.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta